Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Zan auri Fatima da ikon Allah, Inji Isma'il kafinta Basawa

Daga Aisha Suleiman Kaduna Idan masu karatu ba su manta ba akwai wata matashiya mai shekara 20 mai suna Fatima Sulaiman da wani ...


Daga Aisha Suleiman Kaduna

Idan masu karatu ba su manta ba akwai wata matashiya mai shekara 20 mai suna Fatima Sulaiman da wani Aliyu Sunusi Umar, ya takewa kafar dama da mota ranar da ta kammala rubuta jarabawar karshe ta (NECO) a jihar Sakkwato.


Yanzu haka dai an yanke kafar, sai dai ta roki gwamnatin jihar da ta hukunta wanda ya yi danadiyar sakata cikin wannan halin kasancewar shi ba ma dan makarantar ba ne, zuwa ya yi wasa da mota da abokansa da suka kammala jarabawar.

Ana cikin haka ne wani matashi daga kasar Zazzau ya ce shi yanzu yaga matar da zai aura da ikon Allah. Matashin mai Suna Isma'ila Basawa ya baiyanawa wakilimu cewa shi tun ranar da ya ji labari yadda Fatima ta tsinci kanta to tun a ranar Allah ya jefa masa sonta a zuciya.

Isma'il ya kara da cewa bai sami natsuwa ba sai da ya tashi daga Zariya zuwa Sokoto birnin Shehu don su yi ido biyu da Fatima.

To ko me ye ra'ayin Fatima da iyayenta game da wannan matashin?

Tambayar da wakilinmu ya yi wa matashin kenan a halin da ake ciki. Nan take ya kada baki ya ce, "A gaskiya duk da halin da Fatima ke ciki ta gamsu da ziyarar da na kai mata kuma iyayen sun karbe ni hannu biyu tare da sanyawa burina albarka nan take"

Tuni matashi ya karyata zargin da wasu ke masa na cewa ya ga kyaune da Allah ya yi wa Fatimar a zahiri. Ya ce sam! Sam!! Shi Allah ne ya jefa kaunar Fatima a zuciyarsa don haka sai inda karfinsa ya kare.

Matashi ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jiha da su taimaka wajen bin kadi akan wanda ya yi sanadin yanke mata kafarta.

Kuma ya yi godiya ga dukkan mutanen da suka nuna tausayawarsu akan abin da ya faru da Fatima. Ya yi fatan Allah ya bata koshin lafiya.

No comments