Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Akwai Yiwuwar Nan Kusa Cutar Maleriya Za Ta Bace Baki Daya

  Wani rahoto ya bayyana da yiwuwar sabuwar allurar rigakafin zazzabin cizon sauro da jami’ar Oxford ta jagoranci samarwa ta iya tasiri waje...

 


Wani rahoto ya bayyana da yiwuwar sabuwar allurar rigakafin zazzabin cizon sauro da jami’ar Oxford ta jagoranci samarwa ta iya tasiri wajen kawar da cutar daga ban kasa.

Bayan nau’in rigakafin Malaria da kamfanin magunguna na GSK ya samar a bara wanda kuma aka yi gwajin sa kan kananan yara fiye da miliyan guda a Afrika tare da tabbatar da tasirinsa wajen kariya daga cutar ta zazzabin cizon sauro da akalla kashi 60, yanzu haka gwaji ya tabbatar da cewa sabon rigakafin na jami’ar Oxford na da tasirin kashi 77 wajen dakile cutar.

Cutar ta Malaria wadda ke sahun cutuka masu hadari da kuma ke kisa babu kakkautawa, a 2020 kadai sai da ta kashe kananan yara dubu 627 galibi a nahiyar Afrika.

Nau’in rigakafin da jami’ar ta Oxford ta samar wanda aka sanyawa suna R21/Matrix-M shi ne na farko a tarihi da aka taba samarwa wanda ya zarta yadda hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta bukata wajen ganin duk wani magani da za a samar sai ya kai akalla kashi 75 wajen tasiri kan cutar ta Malaria.

An dai yi gwajin wannan magani kan yara 450 masu watanni 5 zuwa 17 a Burkina Faso yankin da Malaria ke haddasa mace-macen yara da akalla kashi 22 cikin 100 inda a wannan shekarar aka samu karancin mace-mace sanadiyyar zazzabin har a tsakiyar damuna bayan da aka bai wa yaran allurar rigakafin sau 3.

No comments