Ƴan bindiga da ba a san ko su waye ba harbe wani Inyamiri ɗan kasuwa, mai suna Ifeanyi a unguwar Sabongari a Jihar Kano. Jaridar...
Ƴan bindiga da ba a san ko su waye ba harbe wani Inyamiri ɗan kasuwa, mai suna Ifeanyi a unguwar Sabongari a Jihar Kano.
Jaridar DAILY NIGERIAN ta jiyo cewa lamarin ya faru da misalin ƙarfe 8:45 na dare a daidai ginin rukunin kantina na Azubros a kan Titin France da ke Sabongari a cikin birnin Kano.
Shaidun gani da ido sun ce ƴan bindigar sun iso wajen ne, sannan su ka harbe shi, inda ya mutu nan-take, su kuma su ka tsere.
"Dama, kana gani ka san shi su ka zo kashewa. Shahararren mai sayar da batira ne a Sabongari ," inji shaidun gani da ido.
DAILY NIGERIAN ba ta samu jin ta bakin kakakin rundunar ƴan sanda ta Kano, Abdullahi Kiyawa ba a lokacin haɗa rahoton.
No comments