Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

An Yi Bikin Yi Wa Mutum 200 Daga APC Zuwa PDP Wankan Tsarki A Zariya

Daga Idris Umar Zariya A cikin makon da ya gabata 'ya'yan jam'iyyar APC sama da mutum 200 suka sauya sheka daga jam&...


Daga Idris Umar Zariya

A cikin makon da ya gabata 'ya'yan jam'iyyar APC sama da mutum 200 suka sauya sheka daga jam'iyyar APC zuwa jam'iyyar PDP a garin Samaru dake karamar hukumar Sabon gari a jihar Kaduna.

Wakiliyarmu na daya daga cikin wakilan kafafen yada labarai da suka shaida yadda taron ya gudana a wannan waje kuma a wannan Anguwa.

Taron dai an yi shi ne a bayan gidan shugaban karamar hukumar Sabon Gari dake Anguwar Mangorori Hayin Dogo Samarun Zariya kuma jigo a jam’iyyar APC ta jihar Kaduna.

Manya masu fada aji ne na jam’iyyar adawa ta PDP ne suka yi wa jama'ar da suka sauya shekar wankan tsarki a wannan taron. 

Da masu sauya shekan wanda galibi matasa ne masu jini a jika ke baiyana dalilinsu na barin jam'iyyar APC a wannan lokaci sun tabbatar da cewa rashin cika alkawari ne kashin bayan komawarsu Jam'iyyar PDP ta bakin jigonsu Kwamared Ibrahim.

Bugu da kari jama'ar sun koka matuka bisa cin amanar da jam'iyyar APC ta yi masu na nuna ko in kula da halin da suke ciki bayan gudummawar da suka ba ta kafin hawanta mulki.

Karshe ne jama'ar suka ce gara su yar da kwallon Mangoro su huta da kuda.

Tuni Jama'ar suka bankawa tsintsiya wuta a tsakiyar taro kana suka daga lema sama alamar komawarsu karkashinta. 

Daga cikin manya bakin da suka karbi mutanen tare da yi masu wannan tsarki akwai Honorabul Wusono ma'ajin jam'iyyar  PDP a jihar Kaduna da Honorabul Kasim Abasko sai Honorabul Sakadadi Babban Daraktan yakin neman kujerar Gwamnan jihar Kaduna Honorabul Isa Ashiru Kudan sai shugaban jam'iyyar ta PDP a karamar hukumar Sabon Gari Alhaji Gambo da sauran manyan baki daga jiha zuwa kananan hukumomi.

Bincike da wakiliyarmu ta yi akan wannan barazana da Jam'iyyar APC ke samu a wannan yankin ya gano cewa matsala ce babba da aka samu a tsakanin manyan 'yan siyasar dake fadin karamar hukumar ta Sabon Garin.

Bincike ya hangi matsalar a bangaren yadda wasu daga cikin masu fada aji na karamar hukumar ta Sabon Garin suka bar hannu daya ne kacal ke sauraran koken jama'ar karamar hukumar ta su maimakon su hada karfi da karfe don cimma nasarar a kowanne bangare.

Da yawa daga cikin 'ya' yan jam'iyyar ta APC sun hada kayansu don arcewa wata jam'iyyar sabida wancan dalilai da suke faruwa. 

Sai dai kuma da yiwuwar su manyan APC na karamar hukumar ta Sabon Gari su farga don magance matsalar da ta kunno kai a wannan yankin.

Amma an yi taro lafiya an tashi lafiya.

No comments