Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Arsenal Ta Faro Gasar Europa Da Kafar Dama Bayan Doke FC Zurich Da Kwallo 2 Da 1

  Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta faro gasar Europa da kafar dama, bayan da ta doke FC Zurich har gidanta da kwallaye 2 da 1. Arsenal ne...

 


Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta faro gasar Europa da kafar dama, bayan da ta doke FC Zurich har gidanta da kwallaye 2 da 1.

Arsenal ne suka fara cin kwallo a wasan ta hannun dan wasan da ya ke yi mata wasa a karon farko, Marquinho wanda ya saka kwallon da Eddie Nketiah ya gara masa.

Sai dai kafin hutun rabin lokaci 'yan wasan Zurich suka farke wannan kwallo daga bugun daga kai- sai- mai tsaron- raga, wanda Mirlind Kryeziu ya buga, bayan rafke Ola Selnaes da Nketiah ya yi.

Ana dawowa hutun rabin lokaci ne kuma, Nketiah ya ci wata kwallo da ta sanya Arsenal a gaba da taimakon sabon dan wasansu, Marquinho.

Yaran na Mikel Arteta za su fafata da PSV Eindhoven a wasansu na 2 a matakin rukuni a gasar cin kofin na Europa a Alhaamis mai zuwa.

No comments