Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Farfesa Abubakar Gwarzo Ya Jajantawa Dalibin MAAUN Bisa Rasuwar Mahaifinsa

  Shugaban Jami’ar Maryam Abacha American University (MAAUN) dake Nijer, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ya mika ta’aziyyarsa ga daya daga cik...

 


Shugaban Jami’ar Maryam Abacha American University (MAAUN) dake Nijer, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ya mika ta’aziyyarsa ga daya daga cikin daliban jami’ar Hafiz Sulaiman bisa rasuwar mahaifinsa, Alhaji Sulaiman Mai Barkono.

Marigayin ya rasu ne a kwanan baya a gidansa dake Bakin Kura Quarters a karamar hukumar Bauchi a jihar Bauchi sakamakon gajeruwar rashin lafiya.

Sakon ta’aziyyar na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Farfesa Gwarzo ya raba wa manema labarai a Kano ranar Laraba.

Farfesa Gwarzo wanda shi ne wanda ya kafa kuma shugaban majalisar gudanarwa ta Jami’ar MAAUN Kano, ya bayyana rasuwar Alhaji Sulaiman Mai Barkono a matsayin babban rashi ba kawai ga iyalansa kadai ba, har ma da jihar Bauchi da ma kasa baki daya.

“A madadin kaina da daukacin ma’aikata da daliban Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijar, ina mika sakon ta’aziyyarmu ga Hafiz Sulaiman, dalibin Jami’ar da ke karatu a sashen ilimin gwaje-gwajen lafiya a matakin aji na 300 bisa rasuwar mahaifinsa, Alhaji Sulaiman Mai Barkono Bauchi,” in ji sanarwar.

Farfesa Gwarzo, wanda kuma shi ne Shugaban kungiyar Jami’o’i masu zaman kansu na Afrika ya jajantawa gwamnati da al’ummar jihar Bauchi bisa rasuwar Alhaji Sulaiman Mai Barkono.

Ya kuma yi addu’ar Allah ta’ala ya bai wa dalibin da dukkannin iyalansa karfin gwiwa da jajircewa wajen jure wannan babban rashi mara misaltuwa.

Ya kuma yi addu’ar Allah Ta’ala ya sanya mamacin a Aljannah (Jannatul Firdaus).

Tuni dai aka yi jana’izar marigayin kamar yadda addinin Musulunci ya tanada a mahaifarsa ta Bauchi a jihar Bauchi.


No comments