Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Ina Iya Bakin Kokarina Amma Ba A Yaba Min -Buhari

  Daga Wakilinmu da BBC Hausa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna damuwa game da yadda mutane ba sa fita suna yabawa da ƙwazon gwamnatins...

 


Daga Wakilinmu da BBC Hausa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna damuwa game da yadda mutane ba sa fita suna yabawa da ƙwazon gwamnatinsa, duk kuwa da ɗumbin ayyukan raya ƙasa da yake ikirarin cewa tana aiwatarwa. Shugaban kasar ya yi wannan furucin ne a jihar Imo, lokacin da ya kai wata ziyarar aiki ta kwana guda,a ranar Talata.

To ko me ya sa ba a ganin kwazon gwamnatin?

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce ya karbi ragamar mulkin Nijeriya a wani lokaci da kasar ta samu kanta a tsaka mai wuya. Adadin man da ƙasar take haƙa ya ragu sosai, farashinsa a kasuwannin duniya ya faɗi ƙasa warwas - mma duk da haka, gwamnatinsa ta san yadda take ƙuƙutawa take aiwatar da ayyukan raya ƙasa da kuma inganta tsaro a Nijeriya. Shugaban ya ƙara da cewa idan wani na kokwanto, to ya tambayi al'ummar jihar Borno don jin yadda aka karya lagon ƴan Boko Haram!Sai dai wani abin takaici, a cewar Shugaba Buharin shi ne yadda mutane ke kau da kai – ba sa yabawa - kamar yadda ƴan magana ke cewa abin kirki bai gaji kare ba - wato ko ya yi ma jifar sa ake yi.

“Daidai wa daida, idan aka yi la'akari da lokaci da ɗan abin da ake samu, wannan gwamnatin ta yi rawar-gani ƙwarai da gaske. "Dole ne na faɗa, saboda waɗanda ya kamata su faɗa ba sa faɗa, kuma ban san dalili ba,” in ji Shugaba Buharin.Wataƙila rashin sanin wannan dalilin ne ya sa shugaban ƙasar ya ari ta ƙadangare, wai da ya faɗo daga sama ya zaɓi ya jinjina wa kansa, ko da wasu ba su jinjina masa ba.

Me jam'iyyun hamayya ke cewa?

A siyasa, jam'iyyun hamayya na cikin gwanayen sa-ido a kan gwamnati. Kuma na tuntubi Sanata Umar Ibrahim Tsauri, mamba na kwamitin ƙasa a PDP, don jin yadda suka ji kalamin Shugaba Buharin. Ya ce: "Zai yi wahala a ce shugaban ƙasa na yin ƙarya, sai dai ƙila a ce abin da shugaban ƙasa ya faɗa ba gaskiya ba ne. "Idan Buhari ya ce ya yi aiki na more rayuwa ga al'ummar Najeriya, to mu jefa wannan maganar a kotun shari'ar al'ummar ƙasa, sai su yanke hukunci, shin gaskiya ya faɗa ko ba gaskiya ba. "Mu a arewa duk hanyoyinmu sun zama idan ka bi su, to kana so ka kashe kanka kenan, abin da kawai Buhari ya gwada, ƙila ana ba shi labari ne don ba ya bin hanyar ƙasar. Idan da yana bin hanyar ƙsar, da ya san cewa idan labari ake ba shi to ƙarya ake masa," a cewar Sanata Tsauri. Ya ƙara da cewa "Mu a wurinmu a jam'iyyar PDP, abin da muke so shi ne Buhari ya mayar da mu yadda ya ɗauke mu."

Yaya masu sharhi ke kallon lamarin?

Sai dai wasu masana siyasa a ɓangare guda na ganin cewa shugaban ƙasar na kokawa ne da yadda wasu muƙarrabansa da kuma magoya bayan jam'iyyar APC mai mulkin ba sa tallata ayyukan gwamnatin tasu. Ko da yake, Mallam Kabiru Sa'id Sufi masanin siyasa a kwalejin share fagen shiga jami'a ta jihar Kano, ya ce wani lokaci akan yi wa jagora watsewar ƴaƴan zabi idan zamaninsa ya tasam ma shuɗewa. "A baya akwai ƙungiyar tallan manufofin shi Shugaba Muhammadu Buhari da suka shahara wajen ƙoƙarin zaƙulo abubuwan da wani sa'in ma ake ganin suna yin zulaƙe.

"To amma dukkansu a halin yanzu za ka ga cewa babu, tun da gwanatin ta nisa ta kuma taho ƙarshe, don haka tunanin kowa ya koma yadda zai ga an yi da shi a sabuwar gwamnati. "Don haka hankulansu sun karkata wajen tallata yan takarar da suke goya wa baya." A watan Fabrairun badi ne ake sa ran za a yi babban zabe a Nijeriya. Kuma sabanin wasu zabukan da aka yi a baya, inda za ka ga 'yan takara na tutiya da ayyukan shugaban kasar, har suna hada hotunansu da nasa - a wannan zagayen kusan ko wa ta-kai-takai yake yi wai gobarar bera. Alamar da ke nuna cewa an riga an ci kasuwa - sai maganar watsewa.

No comments