Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Jami'ar MAAUN Ita Ce Jami’a Mai Zaman Kanta Mafi Inganci - Dan Takarar Gwamnan jihar Kano A NNPP

Dan takarar gwamna a jihar Kano a karkashin jam'iyyar NNPP, Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa Jami’ar Maryam Abacha American ...


Dan takarar gwamna a jihar Kano a karkashin jam'iyyar NNPP, Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya dake Kano ita ce mafi inganci a cikin jami'o'i masu zaman kansu a jihar Kano.

Abba Kabir Yusuf ya ce; “tun bayan kafa Jami’ar a Jamhuriyyar kasar Nijer, jami'ar ke samun ci gaba da daukaka. Kuma ingancinta na kara habbaka. Yanzu kana iya cewa kana da Jami’a mai zaman kanta da ta fi kowacce", ya shaidawa Farfesa Gwarzo.

“Abin sha'awa ne da alfahari a wurinmu. Kuma dama so muke mu ga ta zama mafi kyawu da ingancin da yakamata. Muna kira da a ci gaba da kiyaye wannan ingancin da Jami’ar take da shi. A kuma ci gaba da bunkasa ta”, ya nanata.

Dan takarar gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a 16 ga Satumbar 2022 a yayin da ya kai ziyarar ta'aziyya ga shugaba kuma wanda ya kafa Jami’ar MAAUN Nijer, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo bisa rasuwar Rakietou Hassane Mossi.

Rakietou Hassane Mossi ta rasu ne bayan gajeruwar rashin lafiya a ranar 17 ga watan Agustan 2022 tana da shekara 37, kuma tuni aka binne ta a garinsu dake birnin Niamey na jamhuriyyar kasar Nijer kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Tunda farko Abba Kabir wanda ya samu rakiyar mataimakin dan takarar gwamnan, Kwamared Aminu Abdussalam ya mika sakon ta'aziyyarsa ga wanda ya kafa Jami’ar MAAUN Kano, kuma shugaban Majalisar gudanarwar Jami’ar, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, inda ya ce; “muna maka ta'aziyya bisa rasuwar wannan baiwar Allah Marigayiya Rakietou Hassane Mossi”.

Sannan ya yi amfani da damar wajen taya Farfesa Gwarzo murna bisa karramawar da yake samu da nadin sarautar da yake samu bisa gudummawar da yake bayarwa wajen ci gaban zamantakewa da tattalin arzikin al’umma; “Muna maka fatan alheri akan wadannan rawuna da aka nada maka. Amma babban rawani tunaninka na taimakon al'ummarka. Samar da cibiyoyi na samun ilimi. Kuma muna fatan za ka tsaya kan tsari", inji shi.

Abba Kabir Yusuf ya yaba bisa irin yadda ya ga Jami’ar, inda ya ce tabbas jami'ar abin birgewa ce; “Abu mafi muhimmanci; mun zagaya a cikin Jami’arnan, kuma mun gane wa idonmu. Mun ga irin gine-gine da ci gaban da aka samu, abin gwanin birgewa. Muna taya ka murna", inji shi.

A na shi jawabin, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, wanda kuma shi ne shugaban kungiyoyin jami’o’i masu zaman kansu na Afrika, ya yi godiya bisa wannan ziyarar ta'aziyyar da tawagar ta kawo. Inda ya ce tabbas abin farin ciki ne; “saboda shi rayuwa duk mai rai mamaci ne. Wannan baiwar Allah ta bamu gudunmawa sosai amma Allah ya amsheta. Allah ya gafarta mata yasa ta huta”, ya yi addu'a.

A yayin ziyarar an zagaya da tawagar dan takarar gwamnan wurare daban-daban a cikin Jami’ar wanda ya hada da sashen makarantar Kwamfuta, sashen kimiyyar lafiya da na zamantakewa da gudanarwa da kuma jinya, filin wasa na Ibrahim Yakasai Sport Complex, da dai sauran su.

Daga cikin ma’aikatan gudanarwa na Jami’ar na MAAUN da suka halarci karbar masu ziyarar sun hada da Shugaban MAAUN Kano, Farfesa (Dr.) Mohammad Israr, Mataimakin Shugaba bangaren gudanarwa, Dakta Habib Awais Abubakar da Dr. Aliyu Maringa, Darakta a ofishin wanda ya kafa da dai sauransu. 

No comments