Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Kisan Sani Rai's: Tawagar Shaikh Zakzaky Ta Mika Ta'aziyyarsa Ga Iyalan Marigayin

Daga Hussaini Ibrahim Shehin Malamin Addini Musulunci a Nijeriya, kumaJagoran Harkar Musulunci, Shaikh Ibraheem Zakzaky ya tura ...


Daga Hussaini Ibrahim

Shehin Malamin Addini Musulunci a Nijeriya, kumaJagoran Harkar Musulunci, Shaikh Ibraheem Zakzaky ya tura tawagar wakilansa karkashin jagorancin Malam Nafiu, domin yin ta'aziyya gami da jajantawa ga iyalan Marigayi Malam Sani Ra'is Funtuwa da 'yan bindiga suka yiwa kisan gilla a gidansa da ke Funtuwa.

Wakilan Shaikh Zakzaky, Malam Nafiu ya sami ganawa da Iyaye da iyalai da 'yan'uwan Marigayi Malam Sani Ra'is, inda suka isar da sakon Shaikh Zakzaky na ta'aziyyarsa bisa kisan gillar da aka yi ma shi, gami da jajantawa akan 'ya'yan Marigayin guda biyu (2) da 'yan ta'addan su ka tafi da su.

Da yake amsar gaisuwar, kanin Mahaifiyar Malam Sani Rais, Malam Labiru Funtuwa, ya nuna matukar farin cikinsu da ganin wannan tawaga mai albarka kuma ya mika sakon godiya ga Shaikh Zakzaky da kuma sanya Iyalan Marigayi cikin addu'a dan kubutar da su daga hannan 'yan bindiga.

Daga karshe wakilan sun yi addu'a ga Marigayin tare da fatan Allah (SWT) Ya gaggauta kubutar da 'ya'yan marigayin daga hannun 'yan ta'addan.

A daren Juma'a ne  9/9/2022, 'Yan bindigar suka kai wa Gidan Sani Muhammad Lawal Rais, marubuci kuma manomi dirar mikiya a gidansa dake  Sabuwar Abuja cikin Karamar hukumar Funtuwa jihar Katsina. 'Yan bindigar sun nemi su ta fi da shi Daji shi kuma yaki tafiya ya yi iya kokarinsa wajen ganin ya turje masu wannan ne ya sanya suka fito da shi bayan gidansa suka bude masa wuta suka kashe shi a nan take.

Kisan Sani Rai's Funtuwa da 'yan bindigar suka yi ya girgiza al'umma matuka musamman masu bibiyar rubutunsa da yake yi na fagen ilimin sanin taurari da hisabi da kuma kokarin bayyana ma al'umma wane ne Imamul Hujja (AJ).

Al'ummar Musulmi da kiristoci da makwabtansa zukatansu sun bugu a lokacin da suka samu labarin cewa, 'yan bindigar sun kashe Sani Rais saboda yadda suke amfani da Rubutunsa da kuma tallafi da ya ke ba su da kyakkyawar mu'amalarsa da su.

Marigayi Sani Rais ya kware wajen hada lisafin aka haruffan Al'kurani da wayar wa mutane wasu lamuran da ake shiga dimuwa a cikinsu. Misali kamar sanin su waye Ai'mma a cikin Littafin Baibul wanda Kiristoci ke amfani da shi tsohonsa da sabonsa, sai kuma rubutunsa na baya bayanan na sabuwar shekara ta Musulunci ta 1444, ya yi rubutun akan hijira ta 1444, har mukara ta 14.

A cikin wannan satin, sai kuma rubutunsa na karshen wanda ya saki kafafen sada zumunta wanda ana gobe ne 'yan bindigar za su kashe shi watau ranar Laraba Mai taken "MAKOMAR RAUNANA DA AKE ZALUNTA' . Daga Litafin Imamul Mahadi (A) da labarin gaibu "daga silsilar bayani Sayyid Hassan Nasarullah. Daga shafin na 40 zuwa 46.

Wannan Rubutu na Marigayi Sani Rais shi ne na karshe wanda ya saki domin karuwar al'umma. 

Marigayi Sani Rais mutum ne mai neman na kansa halak wannan ya sanya ya maida hankali wajen noman damuna da na rani da kiwo, duk da baiwar da Allah ya yi masa ta kimiyya da fasaha wajen hada FM tasa a lokacin da ya zamo zakara wajen gyaran rediyo da talabijin.

Marigayi Sani Rais Allah ya amshi ransa ne sakamakon kisan 'Yan bindiga Yana da shekaru 53 a duniya, ya bar mata daya da 'ya'ya sha daya kuma babban dansa ya yi shahada ne a lokacin waki'ar Zariya inda Sojoji suka kashe shi a Gyallesu gidan Sayyid Zakzaky (H) .

Kuma yanzu haka abin da takaici 'yan bindiga sun tafi da yaransa biyu, Mace 'yar shekara 15, da namijin Dan shekara Tara.

Hoton Marigayin

No comments