Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Kungiyar 'Yan Kasuwar Makarfi Ta Jihar Kaduna Sun Koka

Daga Idris Umar, Zariya A cikin wannan satin ne 'ya'yan kungiyar babban kasuwar  Makarfi mai ci duk sati a karamar hukum...Daga Idris Umar, Zariya

A cikin wannan satin ne 'ya'yan kungiyar babban kasuwar  Makarfi mai ci duk sati a karamar hukumar Makarfin ta jihar Kaduna suka koka.

Sheikh Rabi'u Ashara shi ne shugaban kungiyar a wannan lokacin kuma shi ne ya zanta da manema labarai a ofishinsa dake garin na Makarfi.

Wakilinmu na daya daga cikin wakilan kafafen yada labarai da suka ziyarci 'yan kasuwar don jin yadda suke tafiyar da harkokin kungiyar tare da jin kalubalen da kungiyar ta su ke fuskanta.

Ashara ya fara mika godiyarsa ne ga Allah sannan ya yi yabo ga Annabin Rahama Muhammad mai tsira da amimci.

Bayan malamin ya nuna godiya akan ziyarar da kafafen yada labaran suka kawo masa nan take ya amsa wasu tambayoyi  daga wakilan kafafen yada labaran kamar haka;

Ko akwai wani garabasa da kungiyar ta samu a siyasance (romon dimokuradiyya) ganin yadda kungiyar ke bayar da gudummawa a kasa baki daya a bangarori daban-daban musamman tabbatar da adalci a kasuwar mai fitar da amfanin gona ga kasa baki daya.

Sai shugaban ya ce, a gaskiya ya zuwa yanzu babu wani abu da kungiyar 'yan kasuwar Makarfi za su nuna a matsayin taimako daga gwamnati zuwa 'yan siyasar da ake da su a fadin jiha zuwa karamar hukumar har zuwa Tarayya.

Shugaban ya kara da cewa tun abin na damunsu har ta kai ga cewa yanzu ba sa yi wa kowa magana akan su taimakawa kungiyar saboda takaici da ban haushi.

Amma ya nuna kokarin shugaban karamar hukumar Honorabul Mayere bisa kokarin da yake yi a wani lokacin.

Haka zalika shugaban ya yi kira ga dukkan shugaba da cewa ya ji tsoron Allah akan shugabancinsa kamar yadda Allah ya yi umurni da shi.

Ya ce ya kamata dukkan shugabanin dake wannan yankin su hada karfi da karfe wajan karfafa wannan kungiyar don ci gaban karamar hukumar ta Makarfin. Ya ce abin mamaki hakan ya gagara.

Kuma ya nuna takaicinsa akan yadda masu ruwa da tsaki a bangaren tsaro suke sakaci wajen daukar matakai akan wasu bata gari masu fakewa da guzuma suna sarar karsana ya ce, wajibi hukuma su sanya idanu akan duk wani mai kawo barazana a fadin karamar hukumar ta su da kasa baki daya.

Karshe ya ja kunnen 'yan kasuwar da su ji tsoron Allah a yayin da suke harkokinsu. 

Shugaban ya kara da cewa kungiyarsu na nan tana sa idanu akan marasa gaskiya. Kuma ya yi godiya ga 'ya'yan kungiyar masu bin doka da oda. 

Kuma ya yi kira ga manyan 'yan kasuwar da su ci gaba da zuwa siyan kaya abinci don komi na tafiya daidai kamar yadda aka saba. 

Ya kara da cewa yanzu amfanin gona ya zo don haka ya yi fatan Allah ya sa a ga karshen daminar lafiya tare da fatan Allah ya zaunar da kasarmu lafiya.

No comments