Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Matsaloli 7 Da Suka Assasa Tafiyar Shugaban Hukumar Kula Da Ayyukan ‘Yan Sanda, Musiliu Smith

  Rahoton RFI Hausa Bayan murabus din da tsohon Sufeto-Janar Musiliu Smith ya yi a matsayin shugaban hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda ta N...

 


Rahoton RFI Hausa


Bayan murabus din da tsohon Sufeto-Janar Musiliu Smith ya yi a matsayin shugaban hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda ta Najeriya, dalilan da suka kai ga ficewar sa sun fara bayyana.

Ko da yake hukumar, ta bakin kakakinta, Ikechukwu Ani, ya shaida wa manema labarai cewa Smith ya yi murabus ne bisa “batun lafiyarsa”, sai dai sakamakon binciken da jaridar Daily Trust ta gudanar, ya nuna cewa tarin matsaloli da dama ne ya sa aka kore shi.

Smith, wanda aka nada a ranar 25 ga Yuli, 2018, tare da wasu kwamishinoni, ya kamata ya jagoranci hukumar har zuwa 24 ga Yuli, 2023 don kammala aikinsa na shekaru biyar kamar yadda dokokin da suka kafa hukumar suka tanadar.

Sauran kwamishinonin da aka nada a shekarar 2018 tare da Smith da Ogunbiyi sun hada da Lawal Bawa, mataimakin babban sufeton ‘yan sanda mai ritaya (kwamishina da ke lura da, Arewa maso Yamma); Mohammed Najatu (mamba, a Arewa maso Yamma); Braimoh Austin (memba, a Kudu maso Kudu); Rommy Mom, lauya (memba, a Arewa ta tsakiya) da Dakta Nkemka Jombo-Ofo (memba, a Kudu maso Gabas).

Jaridar Daily Trust ta ba da rahoto na musamman kan yadda aka tilastawa Smith yin murabus a yayin wani taron hukumar da aka gudanar a Abuja ranar Laraba, inda aka umarce shi da ya mika shugabancin ga kwamishina na daya wato mai shari’a Clara Ogunbiyi mai ritaya.

Ogunbiyi, wadda ta yi ritaya daga kotun koli, ta fara aiki ne a matsayin mukaddashinsa. Ana sa ran za ta ci gaba da rike mukamin har sai lokacin da shugaban kasar Muhammadu Buhari ya yi wa hukumar nadin sabon shugaba.

Daukar ma'aikata

A daidai lokacin da ake fuskantar hare-hare da dama, laifuka da sauran kalubalen tsaro a shekarar 2018, masu ruwa da tsaki, da ‘yan Najeriya, sun yi kira ga shugaba Buhari da ya kara yawan ma’aikata a rundunar ‘yan sandan kasar.

Jim kadan bayan amincewar da Buhari ya yi a taron Majalisar Zartarwa ta Tarayya na daukar ‘yan sanda 10,000 duk shekara har tsawon shekaru hudu, aikin daukar ma’aikata ya shiga cikin rudani a lokacin da hukumar ‘yan sandan da kuma rundunar ‘yan sandan kowannen su ya dage kan cewa shi ke da alhakin daukar ma’aikata.

Badakalar karin girma

Duk da cewa akwai tsare-tsare na matakan da ke kai ga karawa jami’an rundunar ‘yan sandan Najeriya karin girma, bincike ya nuna cewa hukumar ta ci gaba da sauke nauyin da ke kanta ga ‘yan sanda a karkashin gwamnatin Smith.

Wannan ci gaban, a cewar wasu kwamishinonin da suka zanta da jaridar Daily Trust ba tare da bayyana sunayensu ba, ya haifar da korafe-korafen yadda ake gudanar da ayyuka da kuma rashin samun damammaki a hukumar ‘yan sandan.

Korar jami'an 'yan sanda

A kwanakin baya ne Sifeto Janar na ‘yan sandan Najeriya Usman Alkali Baba ya kori wasu jami’an rundunar bisa kuskuren da ka iya kawo wa rundunar batanci.

A watan Yuli ne rundunar ‘yan sandan Najeriya ta kori wani jami’i mai suna Richard Gele da ke bayar da hujjar karbar kudi a wani faifan bidiyo da ya fara yaduwa a shafukan sada zumunta.

Babban sufeton ya kuma amince da korar wani jami’in ‘dan sanda a Cross River, Liyomo Okoi, bayan an dauki hotonsa a wani faifan bidiyo kwanan nan yana dukan wani farar hula da adda a ranar 31 ga Yuli, 2022.

Gudanar da taron da ba a saba yi ba

Hakazalika, wasu kwamishinonin da suka zanta da Daily Trust sun bayyana cewa a zamanin mulkin tsohon shugaban hukumar, taron nasu da suka yi bai kai sau biyar ba.

Jami’in ya ce, “Bana tunanin taron namu ya kai har sau biyar a zamanin tsohon shugaban. A al'ada, ya kamata mu rika gudanar da taro akai-akai don warware wasu batutuwan da suka dace, amma irin wannan bai taba faruwa ba.

“Wannan batu na daukar ma’aikata bai kamata ya kai matakin da ma’aikata a hukumar za su gurgunta ayyukanmu ba kafin mu saurari kokensu dangane da hakan.

Gyaran Dokar hukumar

Masu ruwa da tsaki a hukumar sun nuna rashin jin dadinsu da wasu sassa na dokar ta hukumar ‘yan sandan, musamman bangaren da ya ce ya kamata Sufeto Janar na ‘yan sanda mai ritaya ya jagoranci hukumar.

Binciken da Daily Trust ta gudanar ya nuna cewa a shekarar 2017, daga cikin shawarwarin da ofishin sake fasalin ma’aikatan gwamnati ya bayar shi ne gyaran dokar da kafa hukumar ‘yan sandan na shekarar 2001.

Shafi na 61 zuwa 71 na daftarin kamar yadda aka samu sun ba da shawarar cewa kada shugaban hukumar ya zama dan sanda mai ritaya.

Zargin badakala da kuma rashin kammala gine-gine

Da yake magana a wani taron manema labarai a makon da ya gabata, shugaban gamayyar kungiyar kwadago reshen hukumar ‘yan sandan, Adoyi Adoyi, ya ce ma’aikata sun yi zargin cewa kujerar da Smith ke jagoranta ta karkata akalar kudaden da aka ware domin kammala ginin ofishinsu.

Ya ce daya daga cikin dalilan da ya sa suka kada wa Smith kuri’ar yanke kauna, shi ne rashin kammala ginin duk da makudan kudade da aka ware domin aikin.

Jindadin ma'aikata

Kusan a kullum, ma’aikatan hukumar na kukan rashin kulawa da hukumomin da ke karkashin jagorancin tsohon shugaban hukumar.

Da yake magana kan lamarin, Adoyi ya ce, “A matsayinmu na kungiyar da ke da alhaki, muna ba da kwarin gwiwa wajen bayyana cewa duk wasu sharuddan da suka dace don ci gaba da aiki sun saba wa hukumar; don haka shirin na ci gaba da tada hankalinmu har sai an cika yarjejeniyar da muka yi a baya.

Hukumar za ta tantance masu neman aikin ‘yan sanda a watan gobe

A halin da ake ciki kuma, hukumar ta ce har yanzu shafin da aka bude wa masu neman aiki, na ci gaba da aiki har zuwa ranar 26 ga watan Satumba, bayan haka hukumar za ta tantance wadanda suka yi nasara.

Ikechukwu Ani, the spokesman of the commission, in an interview with our reporter on Friday, explained that the recruitment was being done in line with the laws of the Federal Character Commission (FCC).

Kakakin hukumar, Ikechukwu Ani, ya bayyana cewa daukar ma’aikatan na yin aiki ne bisa ka’idojin hukumar tabbatar da raba dai-dai ta gwamnatin tarayya.

No comments