Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Mun Gaji Da Yadda Jami'an Tsaron Nijeriya Ke Sace Man Fetur - PENGASSAN

  Kungiyar manyan ma’aikatun mai da iskar gas ta Najeriya, PENGASSAN ta ce, za ta yi fito-na-fito da gwamnatin tarayyar kasar sakamakon gaza...

 


Kungiyar manyan ma’aikatun mai da iskar gas ta Najeriya, PENGASSAN ta ce, za ta yi fito-na-fito da gwamnatin tarayyar kasar sakamakon gazawarta wajen magance gagarumar matsalar satar man fetur a yankin Niger Delta.

Shugaban Kungiyaar ta PENGASSAN, Festus Osifo ya zargi sojojin kasar da sauran jami’an tsaro da satar man fetur din a wata hira da ya yi da  manema labarai a birnin Abuja.

Osifo ya ce, kungiyar za ta dakatar da ayyukanta na samar da man fetur muddin gwamnatin kasar ta gaza daukar mataki.

Wasu bayanai na cewa, PENGASSAN na zargin jami’an tsaron da sace gangan mai akalla dubu 700 a kowacce rana, alkaluman da wani lokacin ke zarta haka a cewarta.

PENGASSAN ta ce, ta gaji da yadda take samar da mai amma kuma jami’an da aka dora wa alhakin kare bututun man suke sace shi.

Shugaban na PENGASSAN ya bukaci gwamnatin kasar da ta cafke tare da garkame jami’an tsaron da ke satar man fetur din a gidan yari, yana mai cewa da dama daga cikin kamfanonin mai sun gaza ci yin karko saboda wannan aika-aikar.

Sai dai a gefe guda, shalkwatan tsaron Najeriya ya musanta wannan zargin da ake yi wa jami’ansa na wawure man fetur a yankin na Niger Delta.

No comments