Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Mutuncin shugabanni zai zube idan ba su daina yi wa al'umma karya ba - Sanata Kwankwaso

Daga Bala Musa Minna Tsohon gwamnan Kano kuma dan takarar kujerar shugabancin Nijeriya karkashin jam'iyyar NNPP, Sanata Inji...


Daga Bala Musa Minna

Tsohon gwamnan Kano kuma dan takarar kujerar shugabancin Nijeriya karkashin jam'iyyar NNPP, Sanata Injiniya Dakta Rabi'u Musa Kwankwaso ya janyo hankalin shugabannin al'umma, wajen rike gaskiya a kowane lamari.

Sanata Kwankwaso ya yi wannan bayanin ne a lokacin ganawarsa da manema labarai a masaukinsa a Minna ranar Alhamis 15/09/22.

Ya ce, "ina kira ga shugagbannin al'umma da na siyasa har da na addini na kowane bangare, da su daina yi wa al'umma karya, don kada nan gaba mutuncinsu ya zube a idanun al'umma. Don a gaskiyar lamari, a yanzu al'ummar Nijeriya suna neman mafita ne. Saboda halin da kasar nan ta shiga na lalacewar abubuwa daban-daban.”

“Ya kamata talakawa su yi taka-tsantsan wajen zaben shugabanni. Saboda sake fadawa irin wannan halin da mutane ke ciki na damuwa. Ya kamata a zabi wadanda ba za su ci amanar mutane ba. Don sau da yawa shugabanni sukan yi karya ne ga al'umma wajen bayyana wa al'umma hakikanin yadda lamarin abubuwa ke tafiya,” in ji shi.

Da yake amsa tambaya a kan lalacewar tsaro a Nijeriya, Sanata Kwankwaso ya ce, "akwai sakacin gwamnati a wannan lamarin. Saboda tana ganin duk abubuwan da ke faruwa ga al'umma. Ya kamata gwamnati da shugabannin tsaro su dauki matakan da suka dace wajen magance wannan matsalar da ke janyo hasarar rayuka da dukiyoyin al'umma. Kodayake hakan ba zai yiwu ba, sai idan gwamnatin Nijeriya tana da bukatar magance wannan matsalar.”

Bugu da kari, a kan ficewar Shekarau daga jam'iyyar NNPP zuwa PDP ya ce, "ba zan so in ce wani abu akan ficewarsa daga jam'iyyar NNPP ba. Saboda wannan ficewar Shekarau daga jam'iyyar NNPP zuwa PDP ra'ayin Shekarau din ne da ya zaba wa kansa, domin yana da damar zaben abin da yake ganin zai dace a gare shi.”

Har ila yau a lamarin takarar shugabancin kasar nan da zaben da ke tafe na shekarar 2023, Sanata Dakta Kwankwaso ya bayyana ra'ayinsa a kan haka, inda ya ce, "kada mutane su zabi wani dan takara a kowane mukami don kudinsa. Ya kamata al'umma ta duba cancanta ne don gujewa matsalolin da za su faru. Saboda mun kafa jam'iyyarr APC don a samu canji na kwarai. Amma kowa yana ganin yadda abubuwa suke faruwa a Nijeriya a yanzu. Abubuwa sun lalace ta ko'ina. 

“Da jam'iyyar APC da PDP duk abu daya ne. Mutanen PDP ne a cikin jam’iyyar APC. Kowanensu ya taka irin nasa salon mulkin. Kowa ya gani. 

“Tunda na yi gwamnan har sau biyu karkashin jam'iyyar PDP a Kano, na yi Ministan tsaro, mai bai wa shugaban Nijeriya shawara a harkokin kasashen Sudan da Somaliya da sauransu. 

“Shi ya sa nasan me yake faruwa a jam'iyyar PDP, wanda ya janyo da ni da wasu mutanen da muke da ra'ayin samun canji na kwarai a Nijeriya, muka kafa jam'iyyar APC. Amma sai ba a samu nasara ko canjin da ake bukata ba don matsalolin sun yawaita ne a kasar nan fiye da lokutan baya,” a cewarsa.

Dakta Rabi'u Kwankwaso ya ce, "a gaskiya ina kiran al'ummar Nijeriya su fahimci cewa, kasar Nijeriya tana da wadatattun kudaden gudanar da duk ayyukan raya kasar nan. Amma rashin iya shugabanci ne yake janyo durkushewar al'amuran kasar nan.” 

Ya ce, "a yanzu jihohin Nijeriya suna fama da matsaloli daban-daban. Noma, harkokin Ibada, kasuwanci, ilmi da sauransu sun gagari mutane. Iyakar gaskiyar lamarin kenan. Amma idan al'umma ta zabe ni a matsayin shugaban kasa karkashin jam'iyyar NNPP, zan yi kokarin gyara abubuwan da suka lalace. Saboda kowa ya san yadda na gudanar da ayyukan ci gaba a Jihar Kano, Ministan tsaro, hukumar NDDC, mai bai wa shugaban Nijeriya shawara a kan yankin Dafur na kasar Sudan da kasar Somaliya da sauran wuraren dana rike. 

“Na yi ayyukan raya al'umma. Kuma na biya duk basussukan da na tarar
a lokacin gwamnatina. Kuma ban bar wa gwamnati bashi ba. Ina bukatar a bincika a duba.
Mun dauki matasa da yawa, 'ya'yan talakawa sama da dubu uku. Muka dauki dawainiyar karatunsu a makarantu na Nijeriya da kasashe daban-daban na duniya. Wadanda suka karanto ilmummuka daban-daban don anfanin al'umma.”

Ya dace mutane su yi wa 'yan takarar mukaman siyasa na kowace jam'iyya tambayar abubuwan da suka yi wa al'umma na ci gaba kafin yanzu. Yadda za su fahimci wane ne ya cancanta, ba yaudara.

A karshe Sanata Dakta Rabi'u Musa Kwankwaso ya yaba wa mutanen Jihar Neja a kan yadda suka tarbi tawagarsa wajen bude hedikwatar jam'iyyar NNPP na reshen Jihar Neja a Minna, ranar Laraba 14/09/22. Haka nan ya washegari Alhamis ya bude ofishin NNPP na Kananan hukumomin Paikoro da Suleja a Jihar Neja kafin komawarsa Kano.

No comments