Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Nijeriya Ta Ce Ta Biya Diyyar Miliyan 289 Ga Wadanda 'Yan Sandan SARS Suka Ci Zarafinsu

  Gwamnatin Nijeriya ta biya 'yan kasar 74 da aka tabbatar da cewar jami'an Yan Sanda, reshen masu yaki da 'yan fashi da makami ...

 


Gwamnatin Nijeriya ta biya 'yan kasar 74 da aka tabbatar da cewar jami'an Yan Sanda, reshen masu yaki da 'yan fashi da makami da aka rusa ta SARS, sun ci zarafinsu diyyar naira miliyan 289. Shugabar Hukumar kare hakkin bil adama ta kasa, Dr Salamatu Suleiman ta gabatar da kudaden ga wadannan mutane 74, inda ta bayyana cewar kafin su an biya wasu 94 naira miliyan 431. 

Suleiman ta godewa wadanda suka gabatar da korafi a gaban kwamitin bincike na musamman da gwamnati ta kafa domin bin Kadin wadanda jami'an 'yan sandan suka ci zarafin su ta hanyar doka. 

Majalisar gudanarwar hukumar ta sha alwashin aiwatar da dokokin da aka kafa ta akai na bin kadin hakkin wadanda akaci zarafin su a kowanne bangare. 

Idan dai ba a manta ba, matasa a Lagos da kuma wasu jihohin Najeriya sun gudanar da zanga zangar adawa da zargin cin zarafin da ake yiwa reshen 'yan sandan da ke yaki da fashi da makami, sanda aka zarge su da kisa da kuma batar ta mutane, abinda ya kaiga lalata kadarorin gwamnati da na jama'a da kuma kai hare hare ofishin 'yan sanda inda aka kashe wasu daga cikin jami'ansu.

No comments