Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Sardaunan Funtuwa Ya Dau Alwashin Magance Bangar Siyasa A Funtuwa

Daga Hussaini Yero, Funtua Daraktan Kamfanin NAK, kuma Sardaunan Funtuwa, Alhaji Akilu Hassan Babayye, ya dau alwashin magance m...


Daga Hussaini Yero, Funtua

Daraktan Kamfanin NAK, kuma Sardaunan Funtuwa, Alhaji Akilu Hassan Babayye, ya dau alwashin magance matsalar bangar siyasa ga matasan Funtuwa.

Sardaunan Funtuwa ya yi wannan kiran ne a lokacin da take amsa tambayoyin manema labarai a ofishinsa dake Funtuwa cikin jihar Katsina. 

Alhaji Akilu Babayye, ya bayyana bakin cikinsa ga matasan Funtuwa masu basira da hazaka wajen karatun da sana'a, amma wasu marasa kishinsu na neman yin amfani da su wajen bangar Siyasa dan amfanin kansu, Inji Sardaunan.

Sardaunan ya yi kira ga 'yan Siyasar Funtuwa da na Jihar Katsina, da su yi koyi da Gwamna Aminu  Bello Masari wajen yaki da bangar siyasa da samarwa matasan abin yi da bangar siyasa ba. Dan duk 'yan siyasar jihar Katsina su shaida ne wajen yadda gwamna Masari ya ke tafiyar da al'umma cikin kwanciyar hankali duk inda zai je ba ya yarda da bangar siyasa.

A kan haka ne Sardaunan Funtuwa Alhaji Akilu ya yi kira ga 'yan siyasar Funtuwa da su ji tsoran Allah wajen tafiyar siyasarsu kuma su yaki tafiya da matasa 'yan bangar siyasa da sunan yaransu.

A karshe Sardaunan ya dau alwashin duk wani matashi mai son ya koyi sana'a ko kuma yana san ci gaba da karatun ya zo wajensa zai taimaka masa don ganin ya zama mutumin kirki da al'umma za ta yi alfahari da shi. Kuma duk dan siyasa da ya kira matasa aka su yi ma bangar siyasa to su fada masa cewa, ya sa dansa ko dan uwansa ya jagorancesu su ganin idan zai yi haka, Inji Sardaunan Funtuwa Alhaji Akilu Hassan Babayye. 

No comments