Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Turmutsitsin Saudiyya: Tunawa da Hajiya Bilkisu Mni

Daga Ammar Muhammad Rajab  Tun a shekarar 2014, rabona da yin sallah (wacce ake cewa babba ko karama) cikin farin ciki da annash...


Daga Ammar Muhammad Rajab 

Tun a shekarar 2014, rabona da yin sallah (wacce ake cewa babba ko karama) cikin farin ciki da annashuwa, a sakamakon jarabawowin da duk suka faru a lokutan sallahn, ko gab. A wannan lokacin da mahajjatanmu suka tafi kasa mai tsarki domin sauke farali, yasa nag a dacewar mu tuna da wannan gwarzuwa, dattijuwa wacce ta rasa ranta wajen bautawa mahaliccinta. 

A shekarar da ta gabata ne (2015), Allah ya yiwa dattijuwa kuma fitacciyar ‘yar Jaridan nan wato Hajiya Bilkisu rasuwa ne, a sakamakon abin da kasar Saudiyya ta kira; ‘TURMUTSITSIN MAHAJJATA’, wanda ya auku a shekarar 2015. Hajiya Bilkisu Yusuf, tana daya daga cikin ‘yan Nijeriyar da wannan ibtila’i ya rutsa da su. Hajiya Bilkisu ta rasu ne a kasa mai tsarki, a kuma lokacin bautawa mahaliccinta. 

An haifi Hajiya Bilkisu Yusuf a ranar 2 ga watan Disaman 1952, sannan ta rasu ne a ranar 24 ga watan Satumban 2015 a Mina, Saudiyyah. Ta rasu tana da shekaru 62 a duniya. Kafin rasuwarta, tana zaune ne a garin Kaduna. Ta rasu ta bar ‘ya’ya biyu, namiji daya mai suna Moshood Sanusi Yusuf sai kuma Mace mai suna Nana Fatima. An santa ne a matsayin fitacciyar ‘yar jarida, kuma mai fafutikar ganin kwato ‘yancin matan da aka danne musu hakkinsu. Ita mai sharhi ce akan al’amuran yau da kullum, kuma ta kafa kungiyoyi daban-daban na  mata a Nijeriya wanda ba na gwamnati ba. 

Ta yi makarantar Firamarenta ne a ‘Ansar Primary School’ dake jihar Kano a shekarar 1964, ta yi Sakandarenta ne a kwalejin gwamnati ta mata dake Dala duk a jihar Kano. Sannan ta yi karatun digirinta na farko ne a jami’ar Ahmadu dake Zariya a bangaren sanin Harkokin Siyasa, sannan ta yi digirinta na biyu a bangaren harkokin Siyasa da sanin sashen Huldar Jakadanci a jami’ar  Wisconsin–Madison a Madison, Wisconsin, dake kasar Amurka. 

Ta sake wani digirin a bangaren aikin jarida  a makarantar aikin Jarida ta ‘Moscow State Institute of International Relations’ a garin Mosko dake kasar Rasha a shekarar 1986. Hajiya Bilkisu ta yi aiki da jaridun ‘Daily Trust’ da ‘kuma Leadership.’ Ta taba zama Editar Jaridar ‘Sunday Triumph’ wacce ake bugata a Kano, a shekarar 1983 zuwa 1987. Sannan har wala yau ta taba rike mukamin Edita a jaridar ‘New Nigerian’ da ake bugawa a garin Kaduna a shekarar 1987 haka zalika a mujallar ‘Citizen Magazine’ da ake bugawa a Kaduna, ta taba rike Edita a shekarar 1990. Ta zama abin koyi musamman ga mata ‘yan Jarida a Nijeriya, ta kuma karfafa mata da yawan gaske wajen shiga aikin jarida. Tana daya daga cikin membobin kungiyar mata ‘yan Jarida ta kasa. Sannan ta yi fice musamman a shafinta na "Civil Society Watch.”

Hajiya Bilkisu, ita ce ta kafa kungiyarnan ta mata wacce ba ta gwamnati ba a Nijeriya wato ‘WIN’. Ta taba zama mai baiwa shugaban Nijeriya shawara akan harkokin da suka shafi kasar waje. Tana daya daga cikin masu fafutikar ganin an kwato ‘yan matan Chibok (duk kafin rasuwarta). Daga cikin kungiyoyin da ba na gwamnati ba da ta da ta kafa ko ta bada gudummawarta sun hada da; WIN, FOMWAN, NIFAAM, HERFON, da sauran su. Rayuwarta ya zama abin koyi na yadda take hidimtawa al’umma da addininta. 

Ta fara auren Alhaji Sanusi Ciroma Yusuf ne, wanda ya taba zama babban jojin Nijeriya, inda suka haifi ‘ya’ya biyu, Moshood Sanusi Yusuf  da kuma Nana Fatima. Bayan sun rabu,  sai ta auri mijinta na biyu wato Mustapha Bintube. Hajiya Bilkisu Yusuf ta rasu ne a lokacin da take jagorantar mahajjata mata a madadin hukumar Hajji ta Nijeriya. Rasuwarta ya girgiza al’ummar Nijeriya da daman gaske. Manya-manyan ‘yan Siyasa, kungioyi daban-daban, hukumomi a Nijeriya, kungiyoyin ‘yan jarida, ’yan Jarida, da kuma Malamai duk sun taya iyalanta ta’aziyyah. Shaikh Ibraheem Zakzaky, jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya, takanas ya tashi tun daga gidansa dake Zariya ya nufi garin Kaduna a inda ya taya iyalanta ta’aziyyah. 

Hajiya Bilkisu Yusuf ta kasance cikin wadanda idan Harkar Musulunci a Nijeriya suka gayyaceta taro, tana zuwa. Taron da ta halarta sun hada; makon hadin kai, ta’aziyya ga Shahidan Kudus sai kuma taron karshe wanda ta halarta na tunawa da Shahidan Kudus a shekarar 2015 (gab da rasuwarta) wanda ya gudana a garin Abuja. Ta gabatar da jawabai a dukkan taron da ta halarta na gwagwarmaya da karfafawa. 

Muna rokon Allah ya Rahamsheta, ya karbi uzurinta, ya sabunta Rahamarsa gareta. Muna rokon duk wanda ya karanta wannan rubutun, ya karanta salatin Annabi, suratul Ikhlas da nufin Allah ya kai ladan ga ruhinta. 

Ammar Muhammad Rajab, 
‘Dan Jarida ne dake zaune a jihar Kaduna. 
14 ga watan Satumban, 2016.

No comments