Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Wani Matashi Ya Yi Wa Masu Son Fatima Raga-raga

Daga Idris Umar Zariya Idan masu karatu ba su mantaba a satukan da ya gabata an samu wasu wanda suka garzaya asibitin da Fatima ...


Daga Idris Umar Zariya

Idan masu karatu ba su mantaba a satukan da ya gabata an samu wasu wanda suka garzaya asibitin da Fatima take kwance don jinyar kafarta da aka yanke sanadiyyar bugeta da mota da wani matashi ya yi a Jihar Sakkwato wanda suka nuna son ta da aure gadan-gadan kamar yadda kafafen yada labarai suka watsa wa duniya.

Ga dai abin da matashi mai suna Sama'ila S Kollo yake cewa a shafinsa na sada zumunta; "Matsalar ita ce har yanzu wasu ba su fahimci ma'anar cima zaune ba  da yake ma'anar cima zaune tana da yawa amma bari mu dauki misalin abin da ya faru a makon da ya gabata na wani Yaro Aliyu sunusi Umar da ya bige wata yarinya 'yar shekara 16 da Mota mai suna Fatima Sulaiman a jihar Sakkwato a cikin munar su ta kammala jarabawar Sakandare (Candy) wanda har ya kai ga Fatima ta zama gurguwa ba tare da ta shirya ba, wannan kaddarar tace.

"Amma da yake mutanan mu sun zama cima zaune, a maimakon su bi
Fatima da addu'ar Allah ya ba ta sauki da yi mata fatan idan laifi ta yi wa Allah ya jarabe ta dan ya yafe mata zunubanta kuma ba haka ba, Allah ya yi haka ne dan ya daga darajar ta dan ta sami tsira ranar gobe kiyama. Amma Ci ma zaunan kasar mu daga jin faruwar haka ba su santa ba ba su san halayyarta ba wasu samari sama da 100 Sakarkaru marasa manufa wadanda zuciyarsu ta mutu murus sun fara tururuwar nuna soyayyar karya gareta da nufin za su Aure ta. Tambayar a nan idan ba dan wata manufa kuke son ta ba, a maganar tsantasar gaskiya ba nakasassu ne a Unguwarku garinku da suka fi Fatima kyau da asali? Ku je ku aure su mana in soyayyar ku ta gaskiya ce ga nakasassu.
Kuma kuna nufin yanzu a ɗaura muku Aure da Fatima saboda tausayi ba za ku kusanceta ba kusantar zaman Aure har sai ta warke? Kun ga wannan karya ce munafuncin samarin soshil midiya ne kawai", inji shi. 

"Muna addu'ar Allah ya karya lagwan duk wani Cima zaunan da ya je dan nuna ma Fatima soyayyar karya wacce bai nuna mata ba a lokacin da tana lafiya. Ya isa a kira ka da mahaukaci idan kaga mutane suna yin abu ba tare da nazari ba da bincike kai ma ka dauka ka ci gaba da yi a matsayinka na mai hankali. Ka sa ni ya kai saurayi mai hankali; jikin ka jikin kane, ba wanda zai inganta maka shi fiye da kai. Ba a hana ƙwaƙwalwa aiki wurin Kawo maka tunanin banza, kada ka manta Allah ya baka zuciya sai ka yi amfani da ita wurin saita al'amuran rayuwarka saboda baka san gobenka ba ya za ta kasance.

"Allah ya ba Fatima lafiya da sauran marasa lafiya gida da Asibiti 
Allah ya kyautata karshen mu mai sako", ya karkare. 

No comments