Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Wani Tsohon Shugaban Hafsan Sojojin Nijeriya Ya Wawure Naira Biliyan Hudu, Inji Shugaban ICPC

Daga Ammar M. Rajab Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC, ta ce akwai wani tsohon shugaban Hafsan Sojin Nijeriya da ya s...


Daga Ammar M. Rajab

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC, ta ce akwai wani tsohon shugaban Hafsan Sojin Nijeriya da ya sace naira miliyan dubu hudu ya sanya su a wani asusun kamfani guda biyu wanda dukkaninsu shi kadai ne mutum daya tilo ke kula da asusun. 

Shugaban ICPC, Farfesa Bolaji Owasanoye shi ne ya bayyana hakan. Inda ya ce daga cikin kudaden satar da shugaban Hafsan sojan ya yi, ya sayi wadansu kadarori a Abuja da sunan iyalai, ‘yan’uwa da kuma abokan arziki. Sannan ya halasta haramtattun kudade. 

Farfesa Bolaji ya ce tsohon shugaban Hafsan sojin a lokacin mulkinsa, ya wawure wadannan kudade ne daga kasafin kudin na soji domin magance matsalar tsaron Nijeriya. 

Shugaban na ICPC, ya ce wani mai Shari’a a Babban kotun kasa ya kawo wa binciken cikas, inda ta bayan fage ya mayar da wadansu kadarorin ga gwamnatin Tarayya a yayin da kuma ya barwa barawon wadansu kudaden da ya sata. 

Farfesa Bolaji har wala yau, ya ce wani abin takaicin kuma shi ne yadda aka karkatar da naira miliyan dubu daya zuwa asusun kamfanin mai na SHELL guda hudu.

No comments