Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

'Yan Bindiga Sun Farmaki Tawagar Kamfen Na Uba Sani A Kaduna, Sun Raunata Mutum Biyu

Jaridar MADOGARA ta labarto cewa;  a jiya Alhamis ne wadansu da ake zargin 'yan bindiga ne suka farmaki tawagar kamfen din d...


Jaridar MADOGARA ta labarto cewa;  a jiya Alhamis ne wadansu da ake zargin 'yan bindiga ne suka farmaki tawagar kamfen din dan takarar gwamna a jam'iyyar APC a jihar Kaduna, Malam Uba Sani. 

Ayokunle Adebayo, daya daga cikin 'yan tawagar ya labart a shafinsa na Facebook cewa; a hanyar komawarsu Kaduna daga Kafanchan inda suka kammala wani zama da shugabanni Kiristoci na Kudancin Kaduna, da wadansu 'yan takarar gwamna a jam'iyyun daban-daban. 

A hanyar dawowarsu zuwa Kaduna a tsakanin Kajuru da Kujama mahara wadanda ake zargin 'yan bindiga ne suka farmaki tawagar, inda suka bude musu wuta kan ababen hawansu, sai dai a cewar Ayokunle Adebayo sun tsira daga harin. 

Sai dai ya ce ababen hawansu uku an lalata su. Inda dole ta sanya suka bar motocin a wurin. Kuma ya tabbatar da cewa biyu a cikin daya daga cikin motocin an raunata da harbin bindiga, kuma tuni aka garzaya da su asibiti. 

Tawagar ta hada da Babban Daraktan kungiyar kamfen din Uba Sani Farfesa Sani Bello, Mainan Zazau, Daraktan kungiyar, Injiniya Namadi, mai bada shawara ga gwamnan jihar Kaduna, Alhaji Ahmed Maiyaki, sai Injiniya Jamil Ahmad Muhammad, mataimaki na musamman ga Sanata Uba Sani, sauran masu bada shawara da jami'an tsaro. 

No comments