Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

'Yan Bindiga Sun Kai Hari Batagawara A Jihar Katsina In Da Suka Sace Mutane Fiye Da 50

  Mazauna kauyen Bakiyawa cikin yankin Batagarawa a jihar Katsina da ke arewacin Najeriya, sun ce suna cikin fargaba da rashin tabbas bayan ...

 


Mazauna kauyen Bakiyawa cikin yankin Batagarawa a jihar Katsina da ke arewacin Najeriya, sun ce suna cikin fargaba da rashin tabbas bayan 'yan fashin daji sun kai musu hari a jiya, al'amarin da ya yi sanadin mutuwar mutum guda tare da sace wasu fiye da 50. 

'Yan sanda sun ce sun aika da karin jami'an tsaro yankin don bukutar da wadanda aka yi garkuwa da su. Wani shaida daga garin na Bakiyawa, ya ce maharan sun je garin ne a kan Babura in da suka aikata wannan aika-aika. Ya ce maharan sun yi ta barin wuta a iska inda suka rika bi gida-gida suna daukar mutane. 

Shi kuwa wani mutum a garin ya shaida wa BBC cewa, 'yan bindigar sun yi kokarin shiga gidansa amma ba su yi nasara ba, inda ya kara da cewa suna dauke da miyagun makaman da 'yan sa kai baza su iya tunkararsu ba. Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Katsina SP Gambo Isa, ya tabbatar da kai wannan hari a kauyen na Bakiyawa da ke karamar hukumar Batagarawa, Inda yace sun yi arangama da 'yan fashin dajin sosai. 

Yankin arewa maso yammacin Najeriya dai, na ci gaba da fama da hare-haren 'yan fashin daji duk da matakan murkushe su da hukumomi ke cewa suna ɗauka, al'amarin da ya jefa dumbin jama'a cikin halin kakanakayi.

No comments