Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

‘Yan Kasashen Waje 286 Sun Samu Takardar Shaidar Zama 'Yan Nijeriya

  Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya ba wa wasu 'yan kasashe waje 286 takardar shaidar zama 'yan kasa. Shugaban ya bukace su da s...

 


Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya ba wa wasu 'yan kasashe waje 286 takardar shaidar zama 'yan kasa. Shugaban ya bukace su da su kasance 'yan kasa nagari. 

A yayin da yake mika musu takardar, ya ce "Kun sadaukar da kawunanku ga Najeriya a lokacin da kuka nuna soyayyarku da biyayyarku ga Najeriyar, a yanzu ita ma za ta saka musu."

Shugaban ya yi bayanin cewa daga cikin mutum 286 da aka ba wa takardar shaidar zama 'yan kasar, 208 daga cikinsu sun karbi takardar da ke nuna cewa daya daga cikin iyayensu ne dan kasar shi ya sa suka zama 'yan kasa, yayin da 78 kuma aka yi musu rijistar zama 'yan kasa. 

Shugaba Buhari, ya bukace su da su rika bayar da gudunmuwa mai kyau ta yadda za a samu ci gaba a kasar, ya ce a matsayinsu na 'yan kasa dole ne su kiyaye da dokokin kasar.

No comments