Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

‘Yan Shi’a Sun Gudanar Da Tattakin Imam Husaini A Tarayyar Nijeriya

Daga Mustapha Muhammad, Salisu Jibril,  Usman Suleiman, Ali Yareema Da Abu Daheerat Kamar yadda suka saba a duk shekara, 'yan'uwa Mu...Daga Mustapha Muhammad, Salisu Jibril, 

Usman Suleiman, Ali Yareema Da Abu Daheerat


Kamar yadda suka saba a duk shekara, 'yan'uwa Musulmi almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky wadanda aka fi sani da 'yan shi'a sun gudanar da tattakin Arba'in na Imam Hussain (AS) a fadin Tarayyar Nijeriya. 

A bana tattakin na su ya fara gudana ne a safiyar ranar Alhamis, inda aka soma gudanarwa a yankuna 6 na Arewacin Nijeriya. 

Wakilinmu ya labarto mana cewa, masu tattakin sun bayyana cewa; "Muna wannan tattakin ne domin tunawa da kwatanta irin wahalhalun da iyalan gidan Manzon Allah (SAWW) suka sha, na tafiya a kasa cikin sahara, babu takalma, daure cikin sarkoki daga Karbala kasar Iraqi zuwa Damashq na kasar Siriya, bayan kisan gilla da aka yi wa Imam Hussain, Dan Sayyada Fatimatuz Zahra, diyar fiyayyen halittta, Manzon Allah (SAWW)", inji su.  

'Yan Shi'ar sun fito ne daga Yankunan Kaduna, Funtuwa, Fambeguwa, Gadar Gayan, Kwanar Malam Mudi (Birnin Gwari), Malumfashi. Wakilanmu sun labarto mana cewa; masu tattakin tattakin daga yankin Kaduna sun hada da 'yan shi'ar da suka fito daga Anguwannin Kaduna, Marabar Jos, da sauran su. 

A yayin da masu tattakin da suka fito daga Funtuwa sun hada da 'yan shi'ar garuruwan Funtuwa, Yankara, Gusau, Talatan Mafara, Birnin Kebbi, Sakkwato, Illela da sauran su. Haka labarin yake a Malumfashi, wanda 'yan shi'ar sun fito ne daga garuruwan Malumfashi, Katsina, Kankara, Kankiya, Dutsin-Ma, Danja, Dabai da kuma Maradin Jamhuriyyar Nijer da sauran su. 

Wakilinmu da ya halarci yankin Fambeguwa, ya ce dubun dubatar 'yan shi'a ne daga jihohin Bauchi, Gombe, Adamawa, Filato, Kaduna suka hau sahun tattakin wanda suka shafe awanni fiye da shida suna gabatarwa. Haka labarin yake a yankin da suka taso daga Gadar Gayan ta jihar Kaduna. 

Wakilinmu da ya ziyarci masu tattakin daga Yankin Birnin Gwari, ya ce a nan ma ya ga dubban 'yan shi'ar sanye cikin bakaken kaya suna tafe cikin alhini da juyayi dauke da bakake da jajayen tutoci suna gudanar da wannan tattakin. 

Kazalika, tattakin ya kuma gudana a birnin Tarayya Abuja a ranar Asabar 17 ga watan Satumbar 2022. Sannan wakilanmu sun labarto mana cewa; irin wannan tattakin ya gudana a garin Zariya da kuma Kano.  

Sai dai duk da kwashe tsawon awanni fiye da 5 a kowanne yanki suna gudanar da tattakin, sun yi lafiya sun kuma kammala lafiya a wannan rana ta Alhamis 15 ga watan Satumban 2022.  

Wakilanmu sun labarto cewa, masu tattakin sun bayyana musu cewa babbar manufarsu ta fitowa shi ne alamta irin wahalhalun da iyalan gidan Manzon Allah (SAWW) suka sha a shekara ta 61 bayan hijira bayan an kashe jikan Manzon Allah, Imam Husaini a filin Karbala, inda aka daure su cikin sarkoki, babu takalma, cikin sahara tun daga Karbala ta kasar Iraki har ya zuwa Dimashk ta kasar Siriya. 

Sannan har wala yau sun ce manufarsu ta biyu shi ne; tunatar da sauran al'umma, Musulmi da wadanda ba Musulmi ba dangane da irin zaluncin da aka yi wa iyalan gidan Manzon Allah (SAW) a tsawon tarihi. 

Wannan ita ce takardar da suka rika rabawa al'umma da manema labarai a yayin tattakin; 

ARBA’IN DIN IMAM HUSSAINI (AS) NA ALAMTA SOYAYYA, SADAUKARWA DA KUMA DAKEWA A KAN MANUFA

Munasabar Arba’in wani aikin addini ne da ake gabatarwa a kowace ranar 20 ga Safar na shekarar Musulunci domin tunawa da kwanaki arba’in da kisan gillan da aka yi wa Imam Hussaini (AS) jikan Manzon Allah (SAWA). An dai kashe Imam (AS) ne a falalen Karbala da ke Iraki a ranar 10 ga watan Al-muharram, shekara 61 Hijiriyya, daidai da 10 ga Oktoba 680 miladiya.

Daga cikin dalilan raya wannan munasaba shi ne tuna irin kunci da wahalhalu da iyalan Annabi Muhammad (SAWA) suka sha sakamakon waki’ar Ashura. Bayan kisan kiyashin da aka aiwatar, an kuma daure mata da kananan yara da sarkoki aka kuma ja su ba tare da ko takalma ba a cikin garjin rana tun daga Karbala har birnin Damascus. Hakika wannan zalunci ne na koli ga iyalan Annabi (SAWA).

Tuni dai masu ziyarar Arba’in na bana suka fara gudanar da Tattaki na kimanin kilomita 100 daga sassa daban-daban na kasar Iraki, misali daga Najaf zuwa Karbala. Jama’a daga bangarorin rayuwa mabambanta, daga sassa daban-daban na duniya, Muslmi da wadanda ba Musulmi ba ne suka samu halarta. Masu aikin sa-kai da dama ne a kan hanyar Karbala suke hidima ga masu Tattaki; kama daga raba abinci da abin sha, bayarwa tare da gyara wuraren hutawa da yada zango ga ilahirin maziyartan.

Yanzu Taron Arba’in shi ne mafi girma a duniya a yayin da adadin dimbin mahalartansa suke nunnunkawa kowace shekara. A halin yanzu, milyoyin mutane daga kusan dukkan sassan duniya ciki kuwa har da Nigeria suna a Karbala domin amsa kiran Imam Hussaini (AS), suna masu nuna tausayinsu da bayyana soyayyarsu ga Manzon Rahma Muhammad (SAWA) da iyalan gidansa tsarkaka bisa wannan mummunan zaluncin da aka yi wa Imam Hussaini (AS) shekaru 1,383 da suka shude.

Irin wannan so da kauna da mabambantan mutane suke nuna wa Imam Hussaini (AS) tare da sadukarwa da kyautatawar mutanen Iraki zuwa ga maziyartan, babban alami ne na yadda ya kamata al’umma su rayu, sai dai kash, abinda aka rasa kenan. Son juna da kyautatawa a tsakanin mutane shi ke haifar dazaman lafiya mai dorewa a doron kasa.

Imam Hussaini (AS) ya sadukar da rayuwar shi ne wurin tunkarar zaluncin Yazidu dan Mu’awuya a yayin da aka yi musu kawanya shi da gomonin mabiyan sa aka kuma yi musu kisan kiyashi a kan filin Karbala. Hakika sun fuskanci matsanancin yanayin takura ciki har da rashin ruwan sha na tsawon kwanaki.

A haka Imam ya jure, ya kuma fuskanci wannan gamayyar rundunar Dan ta’adda Yazidu har zuwa shahadarsa, wanda kafin hakan sai da ya shaidi mummunan wulakancin da aka yi wa mata daga iyalan Annabi (SAWA). Duk wannan sadaukarwar, Imam ya yi ta ne domin karewa da tsamo al’umma daga halin danniya da zalunci. Jajircewa da sadaukarwar wannan muhimmin jarumi, samfuri ce kuma abin koyi domin cimma manufa. Wannan ne kuma ya sabbaba wanzuwar izza da martabar addinin Musulunci kawo yau. Da ba don irin sadaukarwar ba, da tuni Musulunci sai dai a karanta a tarihi.

Kazalika, fafutikar da Imam Hussaini (AS) ya yi, tasirin ta bai takaita ga Musulmi ba kadai, ta yi naso a dukkan duniya. Ta haka ne aka samu muhimman mutane irin su Nelson Mandela da Mahatma Gandhi suka ayyana cewa, lalle sun tasirantu da jimiri da sadaukarwar Imam (AS).

Wani abin lurar shi ne, dakewa da kuma fuskantar zalunci da azzalumai da Imam ya nuna, shi ne tushen duk wani yunkurin kawo sauyi na dawo da martabar Musulunci. Shi din ne har ila yau, sila da tushen gwagwarmayar addinin Musulunci da kawar da zalunci ta Shaikh Ibraheem Ya’qoub El-Zakzaky (H) domin kawo sauyi mai ma’ana a wannan al’umma. Saboda haka, abu ne mai saukin fahimta cewa ba za mu taba mika wuya ga zalunci da danniyar azzalumai ba. Za mu ci gaba da fafutika har ta Allah ta kasance! A karshe muna isar da jajenmu da ta’aziyya zuwa ga Shugaban wannan zamani, Imam Mahdi (ATFS).

Dr. Dauda Nalado

A madadin Harkar Musulunci karkashin jagorancin, Shaikh Ibraheem Ya’qoub El-Zakzaky (H)

Safar 1444 = September 2022

No comments