Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

YANZU-YANZU: An Cafke Tukur Mamu A Misra

Jami'an tsaron birnin Kahira a kasar Masar sun damke mai kokarin sulhu tsakanin yan bindiga da iyalan fasinjojin jirgin kasa...


Jami'an tsaron birnin Kahira a kasar Masar sun damke mai kokarin sulhu tsakanin yan bindiga da iyalan fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna tare da iyalansa. 

Daily Trust ta ruwaito cewa Tukur Mamu na hanyarsa ta tafiya kasar Saudiyya gudanar da Ibadar Umrah yayinda aka tsareshi a tashar jirgin Kahira na kwana guda. 

Rahoton yan kara da cewa gwamnatin tarayya ce ta bukaci a damkeshi. 

A hirar da akayi da shi, ya bayyana cewa bayan gudanar da bincike kansa da jami'an tsaron Masar sukayi, basu sameshi da wani aibi ba.

Mamu ya ce gwamnatin tarayya ta yi niyyar tsareshi kamar yadda aka yiwa mai rajin kafa kasar Yarbawa, Sunday Igboho, amma hakan bai yiwu ba saboda gwamnatin Masar ta tarar dukkan takardunsa sahihai ne. Rahoton ya kara da cewa yanzu haka ana hanyar dawo da shi Nijeriya. 

No comments