Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

YANZU-YANZU: Kotu Ta Umurci ASUU Da Su Janye Yajin Aiki

Kotun masana’antu ta kasa ta umarci Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU), da ta dakatar da yajin aikin da ake yi. A satin da ya gaba...


Kotun masana’antu ta kasa ta umarci Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU), da ta dakatar da yajin aikin da ake yi.

A satin da ya gabata ne gwamnatin tarayya ta maka ASUU a kotun domin daukar matakin da ya dace a kanta kan yajin aikin da ya ki ya ki cinyewa.

A yanzu haka malaman da dalibai sun shafe wata bakwai suna zaune a gida ba tare da ci gaba da daukar darasi ba.

An kai ruwa rana tsakanin gwamnatin tarayya da ASUU kan takaddamar yajin aikin.

Sai dai ASUU ta soki gwamnatin tarayya kan rashin yin abin da ya dace na cika alkawuran da ta daukar mata, don warware yajin aikin.

Tuni masu ruwa da tsaki a fadin Nijeriya suka shiga tofa albarkacin bakinsu kan lamarin, inda ake fatan kawo karshen yajin aikin domin bai wa dalibai damar kowa bakin karatunsu.

No comments