Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Zabar PDP Jihadi Ne A Katsina -Sanata Lado

Dan takarar gwamnan Jihar Katsina a zaben 2023, Sanata Yakubu Lado Danmarke, ya ce jihadi ne a mara wa jam'iayr PDP baya ta lashe zabuka...


Dan takarar gwamnan Jihar Katsina a zaben 2023, Sanata Yakubu Lado Danmarke, ya ce jihadi ne a mara wa jam'iayr PDP baya ta lashe zabukan 2023 a halin da ake ciki a jihar. 

Lado ya bayyana hakan ne a ganawarsa da manema labarai a Karamar Hukumar Safana ta jihar, yayin karbar sabbin 'yan jam'iyar da suka sauya sheka daga wasu jam'iyyu a jihar. Lado ya ce ko shakka ba ya yi cewa PDP za ta samu nasara a 2023 a Jihar Katsinan da tazara mai yawa. 

“Mu a nan Katsina, ba mu da wata baraka ko rarrabuwar kai a PDP. “Na fafata da 'yan takara hudu a zaben fitar da gwanin jam'iyyar da aka gudanar watannin baya, inda na yi nasara. 

“Yanzu haka daya daga cikinsu ne abokin takarata, sai na na ukun da ya koma takarar dan Majalisar Marayya, na hudun kuma yana tare da mu ta hanyar bayar da shawarwari a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.”

No comments