Wanda ya kafa kuma shugaban majalisar gudanarwa na Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya (MAAUN), ya taya daukacin ‘yan Ni...
Wanda ya kafa kuma shugaban majalisar gudanarwa na Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya (MAAUN), ya taya daukacin ‘yan Nijeriya murnar cikar kasar shekaru 62 da samun ‘yancin kai.
Nijeriya ta samu
'yancin kai ne a ranar 1 ga Oktoban 1960 bayan hadewar Arewa da Kudancin kasar.
Sakon taya murnar na
kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban kuma wanda ya kafa Jami’ar ta MAAUN,
Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ya sanya wa hannu, kuma aka rabawa manema labarai
a Kano a ranar Asabar.
Farfesa Gwarzo, wanda shi
ne ya kafa kuma shugaban Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijar ya
kuma taya shugaban kasa Muhammadu Buhari murnar zagayowar ranar samun ‘yancin
kan kasar.
“A yayin da Nijeriya ke
bikin cikar samun ‘yancin kai a yau, ina fatan a madadin Hukumar Gudanarwar
Jami’ar, ina taya daukacin ‘yan Nijeriya murnar wannan gagarumin biki,” in ji
Farfesa Gwarzo.
Ya kuma roki Allah
Madaukakin Sarki da ya ci gaba da yi wa shugabannin kasar nan jagoranci, ya kuma
ba su karfin gwiwa da basira domin kai kasarnan ya zuwa tudun mun tsira.
Farfesa Gwarzo, wanda
kuma shi ne Shugaban Kungiyar Jami’o’i masu zaman kansu na Afrika (AAPU), ya
kuma bukaci ‘yan Nijeriya musamman matasa da su guji shaye-shayen miyagun
kwayoyi da kuma shiga duk wata sana’a mai ma’ana domin ba su damar zama masu
amfani a cikin al’umma ta yadda za su bayar da ta su gudumawa wajen inganta
rayuwar al’umma tare da kawo ci gaban kasa.
Wanda ya assasa Jami’ar
har wala yau ya kuma yi addu’ar samun zaman lafiya da hadin kai tare da
bunkasar tattalin arziki da ci gaban kasa.
No comments