Bankin raya kasashen Afirka da Bankin Musulunci na Duniya da Gidauniyar Bunkasa noma ta duniya za su kashe Dala miliyan 520 a Najeriya dom...
Bankin raya kasashen Afirka da Bankin Musulunci na Duniya da Gidauniyar Bunkasa noma ta duniya za su kashe Dala miliyan 520 a Najeriya domin samar da wuraren da za’a dinga sarrafa amfanin gona a wasu jihohin kasar.
Bankin Afirka zai zuba Dala miliyan 210 a cikin shirin daga cikin kudin, yayin da bankin Islama zai bada Dala miliyan 150 sai kuma Gidauniyar samar da abinci da ta bada Dala miliyan 160.
Jihohin da zasu ci gajiyar shirin sun hada da Cross Rivers da Ogun da Kaduna da Imo da Oyo da Kano da kuma Abuja.
Shugaban Bankin raya kasashen Afirka Akinwumi Adeshina ne, ya kaddamar da shirin a wani bikin da ya gudana a Abuja, inda ya bayyana cewar ta irin wadannan hanyoyi ne kawai za’a bude kofofin inganta noma da kuma samar da abinci.
Adeshina yace matakin farko shine jama’a su yarda cewar, noma kasuwanci ne dake sanya jama’a su mallaki dukiya, ba wai kawai hanyar rayuwa ba.
Shugaban Bankin yace bunkasa harkokin noma ya kunshi samar da na’urorin zamani da inganta hanyoyin kai amfani gona kasuwanni da zuba jari akan kayan more rayuwa musamman kamfanonin da zasu sarrafa amfanin da aka noma.
Adeshina yace yankunan karkara ne zasu ci gajiyar wannan shiri, abinda zai kaiga samar musu da wutar lantarki da ruwan sha da hanyoyin motoci da kuma intanet da zai sa kamfanoni su gina ofisoshinsu a wurin.
Shugaban Bankin yace kai wadannan kamfanonin yankunan karkara zai taimakawa manomawajen rage musu wahalar safarar amfanin gonakinsu da kuma asarar da suke wajen daukarsu zuwa birane.
Adeshina ya bayyana shirin na Najeriya a matsayin mafi girma a Afirka, kuma ya samu goyan bayan ma’aikatun noma da kudi da kuma gwamnonin jihohi.
No comments