Daga Ammar M. Rajab Sha’awa Abdulmumin, mai juna biyu kuma mai ‘ya’ya hudu, ta je Asibitin kwararru na Murtala Muhammad da ke Kano cike d...
Daga Ammar M. Rajab
Sha’awa Abdulmumin, mai juna biyu kuma mai ‘ya’ya hudu, ta je Asibitin kwararru na Murtala Muhammad da ke Kano cike da fatan za ta dawo gida dauke da jaririn da ke harbawa a cikinta watannin baya; amma ba kawai ta rasa jaririn ba, ita kanta ba ta bar asibitin da rai ba.
‘Yar uwarta, Zainab, wacce take tare da ita a wannan tafiya ta azabtarwa, ta yi imanin cewa da a ce asibitin ta bai wa Sha’awa kulawar da ta dace tun ranar 2 ga watan Satumba da ta isa wurin, da an kauce wa wannan mummunan lamari. Ta ce ma’aikatan asibitin sun nuna rashin kulawa da lafiyar ‘yar uwarta.
Bayanai sun nuna cewa jaririn ya rasu ne kasa da sa’o’i 24 bayan Sha’awa ta isa asibitin, amma ba a cire shi a cikin ta ba sai bayan kwana biyu, sa’o’i kadan kafin mahaifiyar ta rasu a ranar 5 ga watan Satumba.
Bisa kididdigar da Asusun Tallafawa Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya wato UNICEF ya fitar, ya nuna cewa Nijeriya ce kasa ta hudu a yawan mace-macen mata masu juna biyu (576 cikin 100,000) sannan kuma a matsayi na biyu a duniya a yawan mace-macen jarirai (69 cikin 1,000).
Zainab da wasu ‘yan jihar Kano da suka nuna damuwarsu sun bayyana cewa mutuwar Sha’awa mai shekaru 30 da jaririnta ire-iren hakan na da yawa kuma za a iya kauce masa. Domin sun yi zargin cewa asibitin ba ya bayar da kulawar da yakamata.
Zainab ta bayyana cewa ‘yar uwarta ta kira ta bayan da ‘ruwanta ya fashe’, amma ta ce ba ta jin ciwon nakuda (wanda aka fi sani da zafin nakuda), a don haka suka yanke shawarar zuwa asibiti.
Lokacin da suka isa wurin, an gano cewa ba wai kawai jaririn ya sauya daga inda yake bane, wanda nauyinsa ya kai fiye da 4kg, jakar da jaririn ke ciki, wanda ke dauke da ruwan da aka ce ya fashe, ya kasance ba ko digon ruwa a ciki, ya zama fanko. A don haka, ma'aikatan kiwon lafiya da ke aiki a lokacin sun yanke shawarar yi mata aiki wato (ECV), wata hanya da kwararrun ma’aikatan kiwon lafiya ke bi wajen ƙoƙarin juya kan jaririn zuwa ƙasa.
Zainab wacce ita ma take dauke da juna biyu ta ce daga nan ne suka ji cewa ma’aikatan asibitin ba su bin tsarin da ya dace ba domin suna ganin kamata ya yi a gaggauta ba su shawarar yi mata tiyata.
“Tun a baya an yi mata tiyata, a don haka duk kankantar matsalar, ykamata ya yi a yi mata tiyatar ‘caesarean’.
“Da safe, sai suka ce mana yaron ya rasu, saboda haka za su je a yi musu tiyata. Daga nan ne suka bukaci a ba ta jakar jini domin a yi mata aikin, wanda a cewarsu zai wadatar saboda tana da isasshen jini a lokacin. Kuma mun saya musu,” inji ta.
Zainab ta ce sun shiga damuwa sosai saboda sa’o’i da dama da aka samar da jinin, ba a yi aikin ba, kuma babu wanda ya zo ya shirya Sha’awa domin a yi mata aiki. Ta kara da cewa a wani lokaci an gaya musu cewa tunda jaririn ya mutu, babu wani gaggawa a cikin lamarin.
A cewarta, a lokacin da ta fuskanci wani likita da ke bakin aiki, sai ya ce mata ko shi ne ya ce a ba su jinin, ya nusasshe da cewa ba zai yi wani aikin ‘caesarean’ ba bayan na uku da ya yi a wannan rana.
“Na ci gaba da binsa cikin dare amma kokarina bai haifar da komai ba. Ita (Sha’awa) ta kwana da mataccen jariri a cikinta. Cikinta ya fara kumburi.
“Ta kasance a asibitin daga ranar Juma’a zuwa Lahadi amma ba a yi mata tiyata ba. A ranar Lahadi ne likitan da ke bakin aiki ya yanke shawarar yin aikin. Watakila likitan ya tausayawa halin da take ciki domin ita mace ce. Ta ce mu kawo jinin. Tun da farko sun nemi ledar jinin, amma a lokacin sun nemi leda daya ne, daga bisani suka nemi leda bakwai saboda jinin da ta zubar.
“Kafin Magriba, aka kira ta da a yi mata tiyata. Bayan sun shigar da ita sai likitar da ta jagoranci tawagar ta fito ta nemi mijinta. Mun san cewa mun sanya hannu kan komai a cikin yarjejeniyar. Ta gaya mana cewa Sha’awa ta wuce matakin da ake tsammani saboda tana cikin wani yanayi mara kyau kuma a sume,” in ji ta.
An dauki kusan mintuna 30 kafin a fito da jaririn da ya mutu, amma gaba daya aikin ya dauki sama da sa'o'i biyar.
Lamarin ya yi matukar tayar da hankali ga Zainab wacce ita ma tana da ciki kusan wata takwas, musamman ganin yadda wasu mata biyu suka rasu a yayin da yayarta ke cikin dakin tiyata.
“Wata mace da ta haifi tagwaye ta rasa ranta a lokacin da take jiran fitowar ‘yar uwata daga daki. Na yi baƙin ciki sosai ganin yadda matar ta mutu,” inji ta.
Bayan an yi wa ’yar’uwarta tiyata, an tura ta zuwa dakin da aka dawo da ita. Ta nuna alamun samun sauki, har ta fara shan shayi, amma da safe Zainab ta dawo daki daga motarsu inda ta kwana, ta hadu da mahaifiyarta tana kokarin tada Sha’awa.
“Daga baya ta fara amai, kuma lokacin da jawo hankalin ma’aikatan jinya da likita, ba su da abin da za su duba ta—babu ‘stethoscope’, babu iskar ‘oxygen’, babu na’urar hurawa da sauran abubuwa.
Lokacin da numfashinta ya fara kasa, sai suka fara tunanin inda za su sami ‘stethoscope’, amma ba su samu ko ɗaya ba. Daga baya suka sami daya a kasa domin dubawa inda suka tabbatar da cewa ta rasu.
“Wannan abu ne mai muni a gare ni. An wulakanta mu, kuma an ɓata lokacinmu, da dai sauransu. A karshe, mun rasa ran ‘yar uwarmu saboda sakaci,” in ji Zainab, yayin da ta yi kira ga al’umma da hukumomi da su taimaka mata ta samu adalci ga ‘yar uwarta.
A makon da ya gabata ne, faifan sauti na kiran neman taimakon ya yadu inda ya zama ɗaya daga cikin bayanan murya da aka fi turawa a WhatsApp.
Za mu tabbatar da adalci - Lauyoyi mata
Jaridar Daily Trust ta labarto cewa; da take mayar da bayani ga wannan kiran, kungiyar lauyoyin mata ta duniya (FIDA), reshen jihar Kano, ta ce ba za su gajiya ba har sai an tabbatar da adalci a shari’ar. Shugabar kungiyar, Bilkisu Suleiman, ta shaida wa jaridar a ranar Asabar cewa, kungiyar za ta gana da Zainab da masu ruwa da tsaki, ba kawai a bangaren shari’a da kare hakkin bil’adama ba, har ma da kungiyar likitocin Nijeriya (NMA) domin duba gaskiyar lamarin da kuma daukar matakan da suka dace.
Haka zalika kungiyar kwararru ta Kano da Jigawa ta yanke shawarar duba lamarin. Bayanai sun nuna cewa kungiyar tuni ta kafa wani kwamiti mai mutane biyar, karkashin jagorancin tsohon shugaban kungiyar lauyoyin Nijeriya (NBA), Abubakar B. Mahmud, babban lauyan Nijeriya (SAN), yayin da fitaccen Farfesa a fannin likitanci, Musa Borodo da tsohon shugaban kungiyar Editocin Nijeriya (NGE), Baba Dantiye, da dai sauransu, suna cikin membobin kwamitin.
Hukumar Kula da Asibitin ta fara bincike
Ya zuwa hada rahoton nan a yunkurin majiyarmu na jin martanin hukumar gudanarwar asibitin kan zarge-zargen bai yi nasara ba, domin babban Daraktan Asibitin, Hussaini Muhammad, bai amsa kira da sakon waya da aka aika masa ba. Sai dai jami’in hulda da jama’a na Hukumar Kula da Asibitin Jihar Kano, Ibrahim Abdullahi, ya shaida wa majiyarmu cewa a ranar Lahadin cewa, tuni suka kafa kwamitin da zai binciki zargin.
Ya ce kwamitin ya fara zama ne a ranar Laraba kuma ana sa ran rahoton kafin karshen mako mai zuwa.
-Rahoton Jaridar HASKEN SHIRIYA tare da hadin guiwar Jaridar MADOGARA.
No comments