Daga Zaharaddeen Gandu An samu labarin cewa, Dantakarar gwamnan jihar Katsina a jam'iyyar PDP Sanata Yakubu Lado Danmarke, tare da ta...
Daga Zaharaddeen Gandu
An samu labarin cewa, Dantakarar gwamnan jihar Katsina a jam'iyyar PDP Sanata Yakubu Lado Danmarke, tare da tawagar shi a ranar lahadin da ta gabata, inda suka ziyarci Babban Ofishin tsohon sakataren gwamnatin jihar Katsina, Dr. Mustapha Inuwa.
Bayan yakai ziyarar a ofishinsa, daga bisani Dr. Mustapha Inuwa yayi ma Lado Danmarke jagora izuwa gidansa, domin tattauna wasu manyan al'ammurra game da zaben shekarar 2023.
Magoya bayan tsohon Dantakarar gwamnan sun yi ma Sanata Yakubu Lado tarba ta musamman, domin nuna jindadin su ga yanda Dantakarar gwamnan yake karrama su tare da Uban gidansu Dr. Mustapha Inuwa.
Tsohon sakataren gwamnatin ya nuna jin daÉ—in shi sosai ga yanda ake karrama shi a jam'iyyar PDP ta jihar Katsina, da ma kasa baki daya.
No comments