Firaministar Birtaniya mai barin gado Liz Truss ta gabatar da jawabin ban kwana ga al’ummar kasar daga fadar Downing Street sa’a guda gaba...
Firaministar Birtaniya mai barin gado Liz Truss ta gabatar da jawabin ban kwana ga al’ummar kasar daga fadar Downing Street sa’a guda gabanin darewar Rishi Sunak kujerar mulki wanda ke matsayin firaminista na 3 da kasar ta gani cikin shekarar nan.
Truss wadda ta shafe makwanni 7 a kujerar mulkin Birtaniya matsayin Firaminista ta nemi yafiya kan matsalar tattalin arzikin da kasar ta samu kanta ciki tare da fatan murmurewa a nan gaba.
Da misalin karfe 11:30 ne Liz Truss za ta gabatar da cikakken jawabin na ban kwana wanda daga nan ne Sarki Charles na 3 zai tabbatar da Rishi Sunak a matsayin Firaminista, nadi na farko da sabon sarkin zai jagoranta.
A cewar Truss matsalar tattalin arziki ta haifar da matsin rayuwa ga al’ummar kasar, kuma ta yi iyakar kokarinta wajen samar da sauki ciki har da saukaka haraji amma halin halin da Duniya ke ciki sakamakon yakin Rasha, dukkanin tsare-tsarenta sun gaza tasiri wajen ceto kasar daga matsala.
Firaministar wadda ta sanar da murabus a radin kanta sakamakon tsanantar matsalolin tattalin arziki da ke barazana ga kasar, ta yi fatan Rishi Sunak mai shekaru 42 masanin tattalin arziki ya taka rawar da ta dace wajen farfado da tattalin arziki.
Sunak wanda zai zama Firaminista na farko da Birtaniya za ta yi wanda ba Bature ba, ya zama shugaban jam’iyyar Conservative ne a jiya litinin bayan janyewar Boris Johnson da kuma yadda Penny Mordaunt ya gaza samun rinjayen kuri’u.
Rishi dan addinin Hindu zai zamo Firaminista mafi karancin shekaru da Birtaniya ta yi cikin fiye da karni 2 da suka gabata.
No comments