A ranar alhamis ɗin data gabata ne 13/October/2022 ƙungiyar kare haƙƙin mata da yara tare da haɗin gwiwar lauyoyi da ke garin Za...
A ranar alhamis ɗin data gabata ne 13/October/2022 ƙungiyar kare haƙƙin mata da yara tare da haɗin gwiwar lauyoyi da ke garin Zariya da kewaye suka fito zanga-zanga akan karen haƙƙin mata da yara. Zanga-zangar na nuni ne da a daina matsa wa mata akan auren dole tare da tofin ala tsine akan masu fiyaɗe.
Wannan zanga-zangar ta samu rakiyar jami’an tsaro mabanbanta. Mun yi ƙoƙarin jin ta bakin ɗaya daga cikin masu zanga-zangar amma haƙar mu bata cimma ruwa ba. Sai dai abin da muka lura masu zanga-zangar suna lurantarwa shi ne a daina matsa wa ƴaƴa mata akan auren dole. Sannan kuma abin kunya ya ƙare ga namiji mai yiwa mata fiyaɗe.
-Daga Mustapha Muhammad wakilin Jaridar Mafita da ke Birnin Zazzau da kewaye.
No comments