Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

An Kashe Mutum 4 A Yunkurin Juyin Mulki A Sao Tome

    Shugaban kasar Sao Tome and Principe kenan, Carlos Manuel Vila Nova.   REUTERS - HANNAH MCKAY An kashe mutane hudu a wani yu...

   Shugaban kasar Sao Tome and Principe kenan, Carlos Manuel Vila Nova. REUTERS - HANNAH MCKAY


An kashe mutane hudu a wani yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba a Sao Tome, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasar ya bayyana a ranar Lahadi.

Sojojin da a ranar Juma'a suka dakile wani yunkurin juyin mulki a tsibirin mai amfani da harshen Portugal da ake ganin tamkar wata fitila ce ta dimokuradiyya, an sanar da cewa an yi asarar rayukan mutane hudu bayan musayar wuta.

Wasu mutane hudu da suka hada da tsohon shugaban majalisar dokokin kasar mai barin gado Delfim Neves, sun yi yunkurin kai hari a hedikwatar sojoji cikin dare, a cewar Firaministan kasar Patrice Trovoada.

Ya ce Neves na daya daga cikin mutane da dama da aka kama, sakamakon zargin hannu da suke da shi a yunkurin juyin mulkin.

Da farko, Trovoada ya ce akwai sojan da aka garkuwa da shi, kuma an ji masa rauni, amma anan sa ran nan ba da jimawa ba zai ci gaba da aikin sa.

Kasar Portugal ce dai ta yiwa Sao Tome mulkin mallaka, wadda ke da yawan al'umma kimanin mutane 215,000 masu fama da talauci, inda suka dogara da taimakon kasashen duniya, amma kuma ana yabawa da tsarin dokokin kasar saboda kwanciyar hankali ta siyasa da kuma majalisar dokoki.

No comments