Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Kotu Ta Dage Shari'ar Cin Zarafi Da Jami'in DSS Ya Yi Wa Matarsa

Wata kotun babban birnin Tarayya Nyanya da ke zaune a Mpape ta dage sauraron karar da ake zargin Shetima Ndula Buba, wani DSS da...
Wata kotun babban birnin Tarayya Nyanya da ke zaune a Mpape ta dage sauraron karar da ake zargin Shetima Ndula Buba, wani DSS da ake zargi da cin zarafin matasa har zuwa ranar 6 ga Disambar 2022.

A yayin da karar ta je gaban mai shari’a Maiwada Inuwa a ranar Alhamis ya dage ci gaba da shari’ar domin a samu damar gurfanar da wanda ake zargi wato
Shetima ga 'yan sanda.

A ranar 22 ga Nuwambar 2021 ne kotun ta umurci DPO na ofishin ‘yan sanda na Wuse da ya binciki ofishin wanda ake zargi bisa laifin cin zarafi, sata, da kuma aikata miyagun laifuka wanda hakan ya saba wa sashi na 264, 286, da 396, wanda ke da hukunci a karkashin sashe na 264, 286. 396 na  Dokar fenal kod.

A wani bangare na umarnin an karanta cewa; "Mai girma Alkalin kotun ya bayar da umarnin a mika batun wannan shari'a ta Zainab Haruna vs Shetima Ndula Buba zuwa ofishinku domin yin cikakken bincike dalla-dalla kamar yadda sashe na 89 (5) na dokar (ACJA, 2015).

"A sanar da kuɗaɗen wannan bincike a gaban kotun nan da makonni biyu ko da ta rahoton Farko ne (FIR)".

Bayan bincike ne ‘yan sanda suka gabatar da rahotonsu tare da sanar da kotu cewa binciken ya nuna cewa a ranar 11/10/2021 da misalin karfe 2030 na safe Shetima Ndula Buba ya samu rashin fahimta da Zainab Haruna wanda a lokacin, matarsa ​​ce, Shetima ya harzuka ya lakada mata duka. 

Rahoton ya kuma kara da cewa an kai wacce ta shigar da karar zuwa asibiti domin karbar magani biyo bayan dukan da ta sha daga wanda ake zargi kuma ta samu raunuka da dama. Haka kuma, an lalata wasu kayayyakin wacce ya shigar da korafin, kamar yadda masu binciken suka lura.

Binciken rahoton ‘yan sanda ya nuna cewa “An shiga da Shetima Ndula Buba kara bisa zargin da aka gabatar, a don haka za a gurfanar da wanda ake zargin a kotu a bisa rahoton farko kamar yadda kotu ta bukata.

No comments