Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

MAKALA: Fashin Baki A kan Fina-finai Da Rubuce-rubucen Batsa

Daga Abdulhadi Aminu (Sidi Abidi) Lamarin kalle-kalle da karance-karancen batsa ya wuce gona da iri a cikin al'umma, abin ba...


Daga Abdulhadi Aminu (Sidi Abidi)

Lamarin kalle-kalle da karance-karancen batsa ya wuce gona da iri a cikin al'umma, abin ban haushi da ban takaici a cikin masu ta’ammali da kafofin na sadarwa an rasa tsayayyun masu faɗa a ji da za su fito su ci gaba da wayar da kan mutane a kan wannan iftila’in da yake neman kassara al’ummarmu, kai wallahi zan iya cewa ma ya kassara mu.

Wallahi abin yana ƙuntata mani, ba ƙaramar damuwa nake shiga saboda lamarin ba, wallahi wani abun ba ma zai faɗu bane, wanda ba ka tunani shi za ka gani da BF a cikin wayarsa, ko kuma in wayarsa ta shiga hannunka a bisa haɗari kuma aka yi gam da katar ka shiga Browser ɗin wayarsa sai ka yi da na sanin shigar wayar hannunka, uwa uba idan ka shiga history na wuraren da ya shiga na browsing, za ka abin takaici da ban haushi, kuma ba mazan ba ba matan ba, ba manyan ba ba yara ba, ba gwagware ba ba ma’aurata ba, kuma kar ma ka min comment cewa baka yi, ban buƙaci in ji hakan ba, kawai ka saurari nasihata.

Su dai waɗannan abubuwan da muke ta kalla na banza, wallahi har yanzu kun kasa gano cewa da BF da American Film duka masana’anta ce take samar da su domin yin business, yadda za a biya actor a film ɗin Action haka za a biya actor na Film ɗin BF, yadda actor na film ɗin India zai je ya biya kuɗi ya sayi kayan ƙarfe domin ya haɗa ƙwanji yadda za a bashi acting a film na faɗa haka actor na BF zai je asibiti ya biya kuɗi a ƙara masa ƙarfin mazakuta ɗinsa saboda da ita yake neman abinci, haka yadda mace take kiyaye jikinta a industry na Bollywood ta hanyar motsa jiki da cin abinci mai gina jiki da sauran abubuwa domin ta kiyaye kyanta da lafiyar jikinta ta yadda za ta samu karɓuwa a wajen directors haka actress ɗin BF take zuwa asibiti ta biya kuɗi a yi mata tiyata a gyara mata mamanta a kuma bata ƙwayoyin sha domin hana maman nata zubewa, haka zalika duk wani private part nata tana biyan maƙudan kuɗaɗe ne a yi mata gyara na musamman da zai janyo hankalin directors na wannan masana’antar su ƙara bata role da zata yi.

Yadda ka san Aminu Saira zai zauna ya yi tunani ya tsara labarin film a Kannywood, haka wani ƙato zai ci ya ƙoshi sai ya tsara labarin film ɗin BF, sai a nemo actors da actresses su zo su buga roll, kowanne a sallame shi ya ƙara gaba.

Saɓanin yadda kuke tunani, BF ba lokaci ɗaya ake tsara shi ba, kamar yadda ake shooting ɗin Kannywood film haka ake shooting BF, in an yi fita ta ɗaya, actor ya yi kuskure a cikin roll da director ya bashi ko actress sai an sake, kuma exactly yadda suke yi a farko haka za su sake maimaitawa.

Bari na baku misali yadda za ku fi fahimta, Idan aka ba actor cewa kalar kwanciya kaza ake so ya yi da matar kuma waje kaza da kaza zai taɓa, to idan ya kuskure bai yi ɗaya daga cikin abinda aka bashi a script ba to sai an sake ɗauka, ko kuma misali ace idan ya tara da ita a daidai lokacin da zai yi inzali ana so ya fitar da gabansa daga gabanta ya yi inzali a waje, idan ya kasa control ɗin kansa ya kasa cirewa a daidai lokacin to sai an sake sabon ɗauka.

Haka mace, idan aka ce ana so misali ta yi kwanciya kaza ko ta yi kalan wasa kaza da namijin a lokacin da yake inzali, idan bata iya yi ba maybe ita ma a lokacin take releasing sai an sake sabon lale!

Wannan yake tabbatar mana da cewa suma ba wai daɗin abinda suke yi suke ji ba, kawai neman kuɗi suke yi da hakan, mu kuma dolaye sai kalla muke yi muna jin daɗi ana ihun banza wai a tunaninmu daɗi suke ji!

Na’am bana kore buƙatuwar namiji ga mace da kuma buƙatuwar mace zuwa ga namiji, domin wannan halitta ce da Allah ya halicce mu da ita, dan haka wannan mu’amalar babu makawa sai an yita, to amma abin damuwar shi ne, yay a kamata a yi, kuma mene ne gaskiya mene ne kuma ƙarya a abinda ake nuna mana a wannan fina-finan?

Da farko tabbas duk halittar da za ka iya gani ga masu wannan sana’ar to da tasirin surgery ko wani special treatment da aka yi musu a wannan halittar, kuma kai ma idan kana so za ka iya mayar da mazakutarka kamar tasu idan za ka iya biyan wannan maƙudan kuɗaɗen da suke biya, haka kema idan kina buƙatar mamanki da sauran private parts ɗinki su zama irin nata to za ki iya biya a yi maki, amma fa ku san wani abu, komin daren daɗewa sai wannan aikin ya dawo baya zuwa ga asalinku, sai dai idan za ku ci gaba da kashe wannan kuɗin ne har ƙarshen rayuwarku to ga fili ga mai doki.

Amma babbar matsala wannan treatment da shan magunguna ɗin ita ce; da farko dai idan ka sha magani da sunan neman ƙarfin mazakuta wai dank a ga wani actor a BF yana da girman mazakuta, ba lallai matarka ta biya maka buƙatarka ba, domin ba z aka gamsu da juriyarta ba, ita kuma in ka matsa mata za ka cutar da lafiyarta, daga nan sai neman mata, idan kuma mace c eke to mijinki ba zai taɓa gamsar da ke ba, daga nan sai neman maza {Allah ya kare mu}.

Ta ɓangaren marasa aure kuma shi ne, ba lallai ne matar da z aka aura ta kasance za ta gamsar da kai ba, haka kema ba lallai mijin ya gamsar da ke ba, kuma wannan ba ƙaramin tasiri yake ba wajen nesantar juna matuƙar ba a samun biyan buƙatar juna a kwanciya, a haka sai abu ya girma a kai ga rabuwa.

Sannan idan ya zamana namiji ya saba da wannan kallon, wallahi idan ba kalla yay i b aba zai samu kwanciyar hankali a ɓangaren sha’awa ba koda kuwa yana da mata, zai zama matar bata da rana haka zai ƙyale ta cikin damuwar rashin biya mata buƙatarta, haka ita ma idan ta saba wallahi mijin ba zai gane komai ba, kuma ba zata samu biyan buƙata ba in dai ba ta wannan hanyar ba.

Abinda ya sanya ba zan taɓo maganar masturbating ba ko kuma istimna’i saboda abu biyu ne a jere, duk wanda yake kallon BF to tabbas yana istimna’i, koda ya kasance ba kowanne ba mai masturbating ne yake wannan kale kallen ba, haka abinda ya sanya ban kawo ɓangaren karanta rubuce-rubucen batsa ba da ake karantawa saboda dukansu aiki ɗaya suke yi a tunanin mutane na biyan buƙata ko kasha sha’awa wai.

Aiki ne mai girma a kanmu, mu guji waɗannan abubuwan ko dan lafiyarmu, haka zalika mu yi ƙoƙarin hana na tare da mu kusantar waɗannan abubuwan ta hanyar tsoron Allah, aure ko azumi, domin waɗannan ne kaɗai katangar kare kai daga faɗawa wannan halakar, Allah ya tsare mu.


To abin tamyar a nan shi ne; Ina matsalar take?

Za ka ga namiji iya namiji, kamili da tsoron Allah da kyautata wa iyaye da maƙwabta, ga taka tsan-tsan da lamurran duniya, amma kuma sai tsautsayi ya haɗa ka da wayarsa ka sha mamaki, haka zalika za ka ga mace kamila cikin hijabi maybe ma har da niƙabi, ga shiga ta kamala iya shiga amma idan gam da katar ya sa ta zo wajanka da wayarta domin ka gyara mata wani abu kuma aka haɗu da la haula sai ka ga abinda zai gigita ka!

Abin ban takaici za ka ga yaro wanda bai wuce shekara 14 ba amma idan ka duba wayarsa za ka yi mamaki musamman idan ka shiga history na visited sites, kuma abin ya zama ruwan dare, wai me ye matsalar ne?

Da farko babu babban abinda yake kawo abin ga yara ƙanana face ɗayan abu uku:

1- Iyayen suna yin mu’amala a gaban yaro irin ta ma’aurata tun yana ƙarami har ya fara fahimtar abubuwa kuma basu sanya kula wajen hana shi ganin abin ba, domin yin hakan yana matuƙar girmar da sha’awar yaro kafin lokacinta ya yi, iyaye mu kula da wannan sosai, yaro a lokacin da ya kai shekara biyu ƙwaƙwalwarsa tana matuƙar haddace abubuwa, kuma abin yana riƙa dawo masa, sai shima ya yi ƙoƙarin gwada abinda ya ga kuna yi.

2- Ko kuma yaron iyaye ba sa bashi kulawa irin wacce ta dace da har zai kasance ƙarƙashin matakan tsaronsu, tare da rashin tsananta bincike a kan lamarin yaron.

3- Ko kuma ya kasance yaron ya haɗu ne da miyagun abokanai, sai su canza masa tunani tare da lalata rayuwarsa ba tare da sanin iyayen ba.

Matakin ɗauka a nan a bayyane yake, iyaye su lura da mu’amalar da za su riƙa yi da junansu a gaban ƴaƴansu, sannan su sanya tsaro na musamman ga yaransu, tare da lura da shige da ficen yaron, abokansa, da wa yake mu’amala, kuma me yake aikatawa a ciki da wajen gida.

Ta ɓangaren manya da basu da aure, mafi yawan abubuwan da suka fi janyo wannan ɗabi’ar su ne:

1- Tunanin cewa hakan zai rage musu sha’awar da ke tare da su, a ƙaramin hangensu shi wannan aikin wai kamar zai taimaka musu wajen danne sha’awarsu.

2- Tunanin cewa hakan zai hana su aikata zina, sai suke amfani da wannan wai a tunaninsu dan magance wannan damuwar da hana kansu afkawa wannan aika-aikar.

3- Tunanin cewa wannan aikin kamar yana samar da lafiya ta hanyar fitar da mataccen maniyyin da mutum ya tara.

4- Shagala irin ta zuciya, tare da jahiltar me ye wannan abin.

5- Rashin sanin illoli da cutarwar wannan aikin.

Da ma wasu dallilai da ban ambata ba, amma dai kusan waɗannan da na ambata gaskiya su ne waɗanda matasanmu suka fi fama da su.

Ta ya mutum zai iya guje wa wannan matsalar?

Da farko dai sai da addu’a, domin fin ƙarfin zuciya abu ne da babu abinda ya fi shi wahala, idan ba da taimakon Allah ba wallahi mutum ba zai iya ba, sannan kuma sai kyakkyawar niyya da aniyar denawa ɗin, domin duk yadda mutum yake son yin abu idan bai yi azama kuma ya dake ba to ba zai iya ba, kazalika mutum ya guji duk wata hanya da zata kai idonsa ko kunnensa zuwa ga abinda zai iya haifar masa da komawa zuwa ga wannan aikin, ta hanyar guje wa shafukan da suke ɗauke da wannan kalar content ɗin, goge duk wani abu da zai iya bijiro da tallar irin waɗannan abubuwan ko kuma taƙaita shafukan a hankali a hankali har mutum ya guje su baki ɗaya.

Sannan abu mai muhimmanci, duk wanda wannan ɗabi’ar ta kama to lallai wallahi yana da buƙatar yin aure cikin gaggawa, domin hakan ne hanya mafi sauƙi kuma mafi sauri wajen fita daga wannan ashha ɗin.

Haka zalika lizimtar azumi yana da matuƙar tasiri, mutum ya tsara wa kansa tsari mai kyau domin yaƙi da wannan mummunar ɗabi’ar.
Idan kuma duk wannan bai yi amfani ba, to mutum ya je na nemi likita ya bashi magungunan taimako domin rage sha’awar, duk da cewa suna cutarwa suma, amma cutarwarsu bata kai ta cutarwar wannan ɗabi’ar mai haifar da cutarwa ga private part ba, cutarwa kuma mai matuƙar wuyar warkewa.

Sannan kuma mutum ya nemi magani, domin wanda yake kale kallen banza tabbas yana aikata istimna’i {masturbating}, kuma mai aikata wanan lallai yana ɗaukar cututtuka da daman gaske, mafi ƙarancinsu shi ne rashin haihuwa da kuma lalacewar al’aura!

Su kuma masu aure, a iya abinda na sani manyan dalilan yin wannan ɗabi’ar a wajensu su ne:

1- Kasancewar tun asali tun kafin aure an saba da wannan ɗabi’ar har ta zamo jiki ta yadda ba za a iya rabuwa da ita ba, hakan yana sa abin ya zama jiki ga mutum, ya kasance kwata-kwata ba a jin daɗin juna a kwanciyar aure, mai wannan ɗabi’ar duk yadda abokin rayuwarsa zai yi ƙoƙari wajen sauke nauyinsa a wannan janibin to shi fa ba zai samu kwanciyar hankali ba sai ya yi wannan ɗabi’a ɗin.

2- Rashin samun gamsuwa daga wajen abokin rayuwa a kwanciyar aure, wanda hakan yana iya jefa abokin rayuwar cikin halin ƙunci da damuwa ta yadda zai kasa jurewa a yanayin da yake rayuwarsa, dan haka sai ya fara aikata hakan koda dama can ba ɗabi’arsa ba ce, duk da wannan mawuyacin abu ne ka samu irin haka gaskiya.

3- Ƙarancin tsoron Allah da son zuciya, wanda za ka ga mutum abokin rayuwarsa yana yi masa komai na rayuwa amma duk da haka yake iya yin ƙarfin halin aikata wannan abin, ba dan komai ba sai dan biyewa son zuciya.

4- Auren dole yana matuƙar taka rawa wajen kawo wannan matsalar musamman ga ƴa mace, kuma musamman ma ace tana ta’ammuli da shafukan sadarwa, kuma tana da ra’ayin irin kalle-kallen nan ko karance-karancen banza.

Domin magance wannan, a dage da addu’a da kuma kyakkywar niyya da guje wa abin, haka kuma a nemi magani, domin mai aure tasirin cutarwar wannan abin yana bayyana a garesa nan take fiye da marar aure, sannan a kula da inda ake shiga a shafukan yanar gizo, a tsaurara matakai wajen kiyaye kai daga hango abinda zai iya kawo tunanin aikata wannan abin, sannan duk lokacin da mutum ya ji cewa yana son yin wannan aikin to ya yi ƙoƙarin tashi daga wajen da yake ya ɗan fita waje ya motsa jininsa, hakan yana taimakawa wajen daƙusar da wannan abin.

Allah ya taimake mu ya sa mu fi ƙarfin zuciyarmu.

No comments