Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Masu zanga-zangar adawa da dokokin Corona sun mamaye kasar Chana

Daruruwan mutane ne suka fito kan tituna a biranen Beijing da Shanghai a ranar Lahadi don nuna rashin amincewarsu da manufar huk...


Daruruwan mutane ne suka fito kan tituna a biranen Beijing da Shanghai a ranar Lahadi don nuna rashin amincewarsu da manufar hukumomin kasar China na kulle saboda da cutar COVID-19.

Daruruwan mutane sun yi zanga-zanga a babbar jami’ar Tsinghua ta birnin Beijing don nuna rashin amincewarsu da kulle a yau Lahadi, da misalin karfe 11:30 na safe ne dalibai suka fara nuna damuwa yayin wannan ganggami.

Mahalarta taron sun rera taken kasa,suka kuma rera wakar "'yanci zai yi nasara, muna son 'yanci", in ji su.

A birnin Shanghai da yammacin ranar Lahadi, daruruwan mutane ne suka taru don gudanar da wani abin da ake ganin tamkar zanga-zangar ce ta yi shiru, kamar yadda wani ganau ya shaida wa AFP, kusa da inda aka yi zanga-zangar sa'o'i kadan da suka wuce.

Masu zanga-zangar rike da takarda da fararen furanni sun tsaya shiru a wurare da dama, in ji mutumin bisa sharadin sakaya sunansa, kafin daga bisani jami’an ‘yan sanda su tashi don share hanyoyin da aka toshe.

No comments