Shugaban Jami’ar FUDMA, Farfesa Armaya'u Hamisu Bichi Ya Aurar Da Ɗansa


Mataimakin Shugaban Jami’ar Gwamnatin Tarayya dake Dutsinma ta Jihar Katsina, Farfesa Armaya’u Hamisu Bichi ya aurar da dansa Usman Armaya’u Hamisu Bichi ga Munira Mukhtar Bala a jihar Kaduna.

An daura auren ne a masallacin Hayin Dogo da ke Birnin Yero a jihar Kaduna a ranar Asabar 12 ga watan Nuwamba, 2022. Ango ya biya sadaki N150,000 ga amaryar. Iyalai da dama, abokai, abokan aiki, da masu fatan alheri ne suka samu damar halartar daurin auren. 

Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, wanda ya kafa kuma shugaban majalisar gudanarwa na Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya ya halarci daurin auren wanda Ali Yusuf Kakaki ya wakilce shi. 

Jama'a da dama wanda suka samu damar halartar daurin auren sun yi amfani da wannan damar wajen taya mataimakin shugaban Jami’ar FUDMA, Farfesa Bichi murnar auren dansa. 

Post a Comment

0 Comments