Rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewar hare-harenta da Operation Hadarin Daji ya kaddamar da jiragen sama, sun yi sanadiyar mutuwar ‘ya...
Rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewar hare-harenta da Operation Hadarin Daji ya kaddamar da jiragen sama, sun yi sanadiyar mutuwar ‘yan bindiga da dama tare da lalata maboyarsu a yankin Karamar Hukumar Maradun ta jihar Zamfara.
TALLA
Daga cikin wadanda aka kashe a yayin hare-haren na ranar 21 ga watan da ya gabata, akwai wasu daga cikin ‘yan bindigar da ke cikin jerin wadanda ake nema ruwa a jallo a kasar irin su Halilu Buzu da Yellow Kano da Alhaji Gana da dai sauransu.
Wata majiya ta ce, bayan samun bayanan sirrin cewa, Halilu Buzu zai yi wata ganawa da wasu kwamandojinsa a yankin Sububu ne, jami'an tsaron Najeriya suka afka musu.
Har wayau, a wani hari da rundunar sojojin saman Najeriya ta kai a ranar 14 ga wannan watan a maboyar kasurgumin dan bindaga Alhaji Gana da ke dajin Karamar Hukumar Giwa ta jahar Kaduna ya yi sanadiyar mutuwar ‘yan bindiga da dama.
Daga cikin wadanda aka kashe a harin dai akwai Musa Balejo da wasu ‘yan bindiga 8, tare da lalata wasu daga cikin kayayyakinsu.
‘Yan ta’addan dai na daga cikin wadanda suka addabi al’ummar yankin Arewa maso yammacin Najeriya.
No comments