Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Ba Zan Manta Da ABU Staff School Ba - Birgediya Janar Usman Lawal Abdullahi

Makarantar ABU Staff School Samaru Zariya sun yi taron tsoffin dalibai mai taken ABUSSAA 2022 HOME COMING.  Wakilinmu na daya da...


Makarantar ABU Staff School Samaru Zariya sun yi taron tsoffin dalibai mai taken ABUSSAA 2022 HOME COMING. 

Wakilinmu na daya daga cikin wakilan kafafen yada labarai da suka halarci taron.

Taron an gudanar da shi ne a babban dakin taro na jami'ar Ahmadu Bello dake harabar makarantar  wato Assembly Hall. 

Farfesa Yahaya Kajuru shi ne shugaban taron. An sami nasarar zuwan tsoffin daliban duk da matsalar tsaro da ake fuskantar a fadin kasa baki daya.

An gabatar da mukaloli daban-daban masu jawo hankali ga taimakon mafarin rayuwa da kawo wa ita makarantar dauki tare nuni ga muhimmancin zumunci da taimakon juna ga dalibai.

Dakta Abullahi ya gabatar da mukala mai jawo hankalin akan muhimmacin koyan kananan sana'ar hannu maimakon dogaro da aikin gwamnati.

Shima Birgediya Janar Usman yana daya daga cikin manyan baki kuma tsohon dalibi a makarantar.

Birgediya Janar a jawabinsa ya nuna jindadinsa sosai ya kuma ce ba zai taba mantawa da ABU Staff School ba domin ita ce ta zama tushe na samun duk wata nasara a rayuwarasa. 

Kuma ya ce zai zanta da shugabannin makarantar na yanzu don ganin ya bayar da gudummawarsa  kuma ya yi kira ga sauran takwarorinsa na sauran bangarori da su zo su hada kai domin kawo ci gaban makarantar .

Birgediya Janar Usman ya yi godiya ga dukkan tsoffin malaman da daliban da ya hadu da su a wannan taro.

Shima tsahon ministan aikin gona Farfesa Sheikh Abdallah Dangi shima kira ya yi ga daukacin tsoffin dalkbai da kar su kuskura su manta da masomar rayuwa.

Kuma ya karkare da kira ga ga dukkan dalibai da su kara kwazo a dukkan inda suke.

Wakilin Mai Martaba Sarkin Zazzau Ahmed Nuhu Bamalli wanda Hakimin Birni da kewaye ya wakiltar, Barista Sambo Shehu Idris shima ya nuna jindadinsa ne sosai da ganin wannan taro kuma ya yi fatan alheri ga hukumar makarantar da tsofin daliban.

An yi taro lafiya an tashi lafiya.

No comments