Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Dan Majalisa Babawo ya hana 'yan siyasa motsi a karamar hukumar Sabon Gari Ta Jihar Kaduna

Daga Idris Umar Zariya A lokacin da ya kamata 'yan takarar jam'iyyu su motsa domin karfafa mabiyansu ta kowanne bangare ...


Daga Idris Umar Zariya

A lokacin da ya kamata 'yan takarar jam'iyyu su motsa domin karfafa mabiyansu ta kowanne bangare wanda hakan shi zai ba su kwarin guiwar mara masu baya wanda hakan shi zai ba su damar samun nasara a lokacin fafata zaben dake tunkaro su na shekarar 2023 a madafu daban-daban.

To a karamar hukumar Sabon Gari ta jihar Kaduna lamarin ya canza salo. Jaridar Hausa Leadership ta yi nazari akan hakan kuma ta hango cewa a wannan lokacin da guguwar siyasa ke bugawa babu wani dan takara daga kowacce jam'iyya da yake yin motsi a siyasance sai Honorabul Garba Datti Muhammad Babawo wato Dan majalisar tarayya mai wakiltar karamar hukumar Sabon Gari a jam'iyyar APC ta jihar Kaduna.

Tambaya shin ko me ya kawo hakan duk da zaratan 'yan siyasan dake a wannan karamar hukumar da ake alfahari da su a jihar kaduna da kasa baki daya?

Amsar ita ce yadda Dan majalisar ke gudanar da aiki ba kowanne Dan siyasa zai iya yin hakan ba.

Hakan yasa duk' yan takarar da suke a karamar hukumar manyansu da kananansu guiwarsu ta yi sanyi a siyasance a dukkan  sauran jam'iyyun da suke motsi a wannan karamar hukumar wanda ke nuna cewa kamar sun gaza a siyasance.

Hakan yasa sun zura mashi idanu yana ta kwashe masu jama'a babu ji babu gani ba kuma yadda za su yi.

Daga cikin abin da shi Honorabul Babawo ya dukufa akansu a wannan lokacin sun hada da karbar koken jama'arsa manya da kanana musamman abin da ya shafi jindadi da walwalar mutane daga kowacce jam'iyya indai ka kawo kuka to zai kalleka kuma zai kalli koken naka hakan yasa ya zama na kowa a halin yanzu.

Tuni a cikin satin da ya gabata ma ya tallafawa mutane da suka kai 700 da ilmi a bangarori daban daban gami da ba su kudin jari domin dogaro da kai.

Dan majalisar ya gwangwaje matasa masu yawa da horo akan sanin ilimin na'ura mai kwakwalwa tare da mallaka masu guda-guda don karfafa su a zamantakewar rayuwa.

Haka zalika ya mikawa wani masallaci kungiyar Izalatul Bi'di'a wa Ikamatussunah a garin Basawa naira miliyan daya don ci gaban da karasa gininsa bugu da kari duk a cikin wannan satin ya sadaukar fa mota sabuwa kirar OPEL ga kungiyar Fitiyanul Izlam reshen karamar hukumar Sabon Gari.

Kuma mun sami tabbacin ya bai wa kungiyar Nisa'us Sunna reshen karamar hukumar Sabon Gari mota sabuwa kirar OPEL. 

Hakan yasa da yawan mutane ke ganin zai yi wahala wata jam'iyya ta iya kayar da jam'iyyar APC a kowacce kujera a karamar hukumar Sabon Gari ta jihar Kaduna amma lokaci ne alkali.

No comments