Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Farfesa Adamu Gwarzo ya jajantawa Sanata Wamakko kan Rasuwar Matarsa

  Shugaban Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijer (MAAUN), Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, ya jajantawa Sanata Aliyu Wamakko, Mag...

 


Shugaban Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijer (MAAUN), Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, ya jajantawa Sanata Aliyu Wamakko, Magatakardan Wamakko bisa rasuwar matarsa, Hajiya Atika.

Sakon ta’aziyyar na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Farfesa Gwarzo ya sanya wa hannu kuma aka rabawa manema labarai a Kano a ranar Litinin.

Farfesa Gwarzo, wanda shi ne wanda ya kafa kuma shugaban hukumar gudanarwa na Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya, (MAAUN), ya bayyana rasuwar Hajiya Atika a matsayin babban rashi ba kawai ga danginta kadai ba har ma da daukacin al’ummar jihar Sakkwato.

“Samun labarin rasuwar matarka, Hajiya Atika ya yi matukar girgiza mu.

“A madadin iyalina da Jami’ar Maryam Abacha American University (MAAUN), ina mika sakon ta’aziyyarmu a gare ka bisa rasuwar matarka.

“Ina kuma so in yi amfani da wannan dama wajen jajantawa daukacin al’ummar Jihar Sakkwato bisa wannan babban rashi da aka yi, Allah Madaukakin Sarki ya ba ku da sauran iyalai baki daya hakurin jure wannan rashi mara misaltuwa.” Inji Farfesa Gwarzo a cikin sakon ta’aziyyar.

Farfesa Gwarzo, wanda kuma shi ne Shugaban Kungiyar Jami’o’i Masu Zaman Kansu na Afrika (AAPU) ya yi addu’a ga Allah Madaukakin Sarki da ya gafarta mata kurakuran ta, ya kuma sanya ta a Aljannah Firdausi.

Allah ya jikanta da Rahama ya sa ta huta, Amin.

No comments