Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

MAKALA: Gurɓacewar tarbiyyar matasa: Wasiƙa zuwa ga iyaye!

Daga Abdulhadi Aminu Assalamu Alaikum. Wannan saƙo ne daga gare ni zuwa gare ku mahaifana, na tabbata yana da matuƙar muhimmanci...


Daga Abdulhadi Aminu

Assalamu Alaikum.


Wannan saƙo ne daga gare ni zuwa gare ku mahaifana, na tabbata yana da matuƙar muhimmanci ku karanta shi da zuciyar fahimta, kuma ku yi dogon nazari a kan wannan zancen, ku ɗauke shi a matsayin abinda zuciyata take faɗa muku ba wai bakina ba!

Mahaifana!

Mun wayi gari a cikin wani zamani mai cike da ruɗu da hayaniya mai rusa tarbiyyar manya da yara, maza da mata, matasa da dattijai, abin da ya sanya ake ta samun matsaloli masu muni a alaƙar tsakanin namiji da mace.

Yanzu manya da yara maza da mata tunaninsu ya riga ya karkata ne a abinda ya shafi alaƙar namiji da mace cewa babu wata mu'amala tsakanin namiji da mace in ba mu'amalar jinsi ko kwanciya ba, wannan tunanin tsari ne na turawa da suka yi shirin daƙushe tunanin al'umma da kuma raunata ilimi da sanin ya kamatansu domin ci gaba da mulkarsu har a cikin tunaninsu.

Shahararren abu ne a wajen  masu mulkin mallaka cewa, matuƙar kana son ka mulki al'umma to dole ne ka fara lalata tarbiyyar cikin gida wato family, sai ka lalata musu tunanin yadda suke kallon zamantakewa, sai ka sanya musu wani tunani da yake rinjayarsu da shagaltar da su daga yin tunani a kanka, idan kuma kana son family ya yi saurin rushewa to kawai ka lalata tarbiyyar mace, idan ka kasa lalata tarbiyyarta kuma to ka yi ƙoƙarin hana ta tsayuwa da ayyukanta na uwa.

Rubuce-rubuce kokuma fina-finan batsa shi ne babban tsarin yaƙin ruwan sanyi da turawa suka ƙirƙira domin lalata tarbiyyar family in general, da kuma tarbiyyar mace musamman, shi wannan tsarin ya fara samo asali tun ƙarni na sha bakwai a ƙidayar miladiyya a shekarar 1748, wanda wani mutum mai suna Fanny Hill ɗan ƙasar Ingila ya fara rubuta littafin novel na batsa na farko, wanda a lokacin ma hatta gwamnatin ƙasa sai da ta haramta mallaka, siya da siyar da littafin tare da sanya doka mai tsanani ga duk wanda aka kama da littafin saboda hatsari da matsalolin da ta hango ga al'ummarta na ɓangaren tunani da kuma shirin ruguza al'umma baki ɗaya.

Tsarin ya ci gaba da tafiya ta hanyar samar da waɗannan rubuce rubucen har zuwa ƙarni na sha tara, inda aka fara samun wannan abun a matsayin shirin film bayan da aka samu fasahar ɗaukar hoto mai motsi, har dai zuwa wannan lokacin abin yana daɗa mamaye duniya.

Tsarin yin wasan kwaikwayo na bayyana tsiraici da mu'amalar jinsi tsakanin namiji da mace daɗaɗɗen abu ne a cikin al'ummar Rumawa da wasu sassa na turai kamar girka da faransa, amma a tarihin Africa babu wannan mu'amalar da sunan wasan kwaikwayo.

Ya mahaifana masu daraja!
Na yi wannan shimfiɗar ne saboda in sanar da mu haɗarin da wannan masana'antar ta fina-finai da rubuce-rubucen batsa a taƙaice.

Nasarar masu shirya wannan fina-finan ta bayya a zukatan matasa da ma dattijai maza da mata na al'ummarmu, saboda rahoton PornHub babban shafin masana'antar fina-finan batsa ya tabbatar da cewa a shekarar 2021 zuwa yau Nigeria ce ƙasa ta farko a kallon fina-finan batsa, Ghana maƙociyar Nigeria ɗin kuma ita ce ta biyu!

Ba burina tsawaitawa a wannan babin ba, abinda nake so shi ne ku fahimci abinda ke yawo a ƙwaƙwalwata, ku fahimci ina matsalar ta samo asali da kuma warwarar zaren domin gujewa matsaltsalu da suka addabemu na zinace-zinace da ayyukan ash'sha.

To amma me ya janyo wannan karkatar da al'ummarmu ta yi zuwa ga wannan aikin?

Da farko, zamaninmu ya bambanta da zamaninku ya Mahaifana, ginin jiki da ƙirarmu daban da naku, kuma babu abinda zai sa mu zamo ɗaya ta kowanne fanni.
Mafi yawan abincin da muke ci yanzu abinci ne mai matuƙar gina sha'awa da motsata a cikin ƙanƙanin lokaci, abin sha kuma dama abu ne mai matuƙar cakuɗuwa da sinadaran girmama sha'awa da kuma kassara tunanin yaro, dukkan abinda jikinmu ya ginu da shi ba komai bane face zallaln abinci mai kusanto da girman yaro da bashi ƙarfin sha'awa, a taƙaice zan iya cewa maganaɗisun sha'awa ne!

Kun ga jikinmu da wannan abincin ya ginu, yanzu mun girma, muna jin tasirin wannan abincin da muka girma ta dalilinsa, kuma muna fama da wannan tsananin sha'awar da jikinmu ya ginu a kanta, ba wai son ranmu bane ya mahaifana! Wallahi jikinmu ne a haka!

A lokacin da ya kamata ku bamu kariya a kan sarrafa sha'awarmu cikin ɗa'ar ubangiji, sai kuma kuka barmu da son zuciyarmu da kuma ƙaramar ƙwaƙwalwarmu da bata san komai ba sai wannan sha'awar da ta ginu a kai, kun kasa jan hannunmu domin shiryar damu, kun tauye hannu sosai wajen bamu abinda zai yi daidai da ƙirar halittar da kuka ɗora mu a kai!

Muna ƙoƙari duk da haka wajen samun rufawa kanmu asiri ta hanyar yin aure da kare al'aurarmu, amma a wannan lokacin kuma sai kuka tsananta mana lamarin aure, ta kai idan mutum ya furta kalmar aure zai yi to kamar ya taro wa kansa faɗa da duniya baki ɗaya!

Mahaifana!

Ƴaƴanku mata kuma, suma kamar dai mu mazan haka suke, dukkan ƙirar jikinsu da namu da irin abinci ɗaya dai ta ginu, maimakon ku taimake su wajen kare kansu ta hanyar sauƙaƙa lamarin aurensu, kun fifita ku aurar da su ga mai ƙyale-ƙyalen duniya da ku baiwa talaka, kun fifita idan kun yi musu aure baƙin ciki ya kashe su, kun fifita shaiɗan ya ribace su ya ingiza su yin zina alhali suna da aure! Kun fifita su riƙa mu'amala da samarinsu da kuka ƙi bari su aura alhali suna ɗakin aure!

Shin me za ku gaya wa Allah a kan haƙƙinmu da ke wuyanku? Shin Allah zai ƙyale ku? Shin kuna ganin abinda kuke aikatawa daidai ne?

A lokacin da kuka hana mu kame kanmu daga faɗawa halaka, sai kuma aka samu wannan turawan suka bijiro mana da abinda yake daidai da buƙatar zuciyarmu, suka riƙa ribatar zukatanmu da kuma jikinmu wajen bayyana mana abinda zuciyarmu ke ɗauka jin daɗi ne!

Rayuwar duniya ya ku mahaifana faɗa ne tsakanin rundunar shaiɗan da son zuciya da rundunar Allah mai horo da alkhairi, wani lokacin idan mun iya kare kanmu daga kalle-kallen banza, kuna tunanin wani lokacin za mu iya? Wanda da ace kun sauƙaƙa mana da hakan bata faru ba!

Mahaifana masu daraja!
Bani da buri a rayuwata da ya wuce na faranta muku rai, bani da nufin sanya ku cikin yanayin ɓacin rai da ƙunci, saboda na san kun yi ɗawainiya kun sha fama da ni, kuma babu abinda zan yi na iya sauke haƙƙinku da ke kaina, kamar yadda kuma na san babu abinda kuke da buri face ku ga na rayu rayuwa mai kyau, mai cike da farin ciki da yiwa ubangiji ɗa'a, na sani ba burinku cutar da ni ba ko kaɗan.

Ya mahaifana!

Ni ɗan adam ne kamar kowa, zan iya yin dai-dai kuma zan iya yin kuskure, kamar yadda ruhin yi muku biyayya yake tare da ni haka zalika a hannu ɗaya kuma akwai wata zuciya mai horo da mummuna da ke ingiza ni zuwa ga aikata abinda baku tarbiyyantar da ni da shi ba, wani lokacin idan na yi nasara mahaifana wani lokacin ban san me zai faru ba!

Ni wani nauyi ne da Allah ya ɗora muku a rayuwar duniya, kuma ku abin tambaya ne a kan irin kariyar da kuka bani daga faɗawa tarkon son zuciya, ina gama ku da Allah, ku zamo sanadin tsirar imanina da rayuwata wajen katange ni daga faɗawa wannan halakar da ke neman kassara imanina da ruhina!

Mahaifana masu daraja!

Na san za ku iya cewa in lizimci azumi hakan yana kawo maganin wannan abin da yake damu na! 

Gaskiyar Magana azumi ba abinda yake yi a wannan zamanin na daga rage wannan lamarin, saboda a haka jikina da duk ɗan zamanina ya ginu, bani da wannan ƙarfin danne abinda ke takura min ta hanyar azumi, ba kuma ina yi muku ƙarya ba ne, wallahi gaskiya nake faɗa muku.

Idan kuna ganin la'alla ban yi hankalin da za ku min aure ba, to ku dubi ɓangaren halakar da zan iya faɗawa sanadin rashin yin hakan, kuma ku tuna cewa magabata da ƙananun shekaru iyayensu suke yi musu aure domin hana su afkawa wani tunani na daban da zai iya sabbaba samun irin matsalar da muke fama da ita a wannan zamanin, ɗan abin da kuke ganin ban sani ba a game da zamantakewar aure, ku zaunar da ni ku sanar da ni, ku fahimtar da ni ku ceci rayuwata!

Fatan za ku yi nazarin maganata, ina ƙaunar ku mahaifana!

No comments