Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Masarautar Gwantu Ta Bai Wa Gwamna El-Rufai Da Mataimakiyarsa Sarautar Garkuwan Gwantu Da Gimbiyar Gwantu

Daga Muhammad A. Dalhatu Sarkin Gwantu Malam Balarabe Abdullahi Karma ya bai wa Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmed El-Rufai sarautar Ga...Daga Muhammad A. Dalhatu

Sarkin Gwantu Malam Balarabe Abdullahi Karma ya bai wa Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmed El-Rufai sarautar Garkuwan Gwantu inda kumaya bai wa mataimakiyarsa Dr Hadiza Sabuwa Balarabe sarautar Gimbiyar Gwantu.

Basaraken ya sanar da nadin ne a ranar Alhamis din da ta gabata bayan an yi masa nadin sarauta tare da kuma mika masa sandar fara aiki da Gwamnan ya yi a Gwantu, hedikwatar karamar hukumar Sanga.

A jawabinsa yayin bikin nadin sarautar, Sarkin Gwantu ya godewa Gwamnan bisa ayyukan da gwamnatinsa ke aiwatarwa a karamar hukumar, inda ya bayyana shi a matsayin ginshikin da ya samar da tagwayen Sarakunan Gwantu da Arak.

Ya jaddada cewa tabbas samar da masarautun guda biyu zai taimaka matuka gaya wajen kawo ci ga al’ummar dake karkashin masarautun. 

Malam Karma har wala yau ya yabawa mataimakiyar gwamnan jihar ta Kaduna, wanda ya ce tana daga cikin ‘ya’yan masarautar wanda ta kasance mai biyayya ga gwamnan, wanda kuma masarautar ke alfahari da ita. 

Al’ummar Gwantu sun yaba tare da jinjinawa bisa bai wa gwamnan sarautar Garkuwan Gwantu tare da bai wa mataimakiyarsa sarautar Gimbiyar Gwantu, inda suka ce an saya iri a gurbinta. 


No comments