Daga Muhammad A. Dalhatu Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya bukaci daukacin Sarakuna da masarautun jihar da su yi kokarin sa...
Daga Muhammad A. Dalhatu
Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir
El-Rufai, ya bukaci daukacin Sarakuna da masarautun jihar da su yi kokarin samar
da zaman lafiya da hadin kai da shiga ayyukan al’umma domin kawo ci gaba mai
dorewa.
Gwamnan ya bayar da wannan shawarar ne a
yayin bikin nadin Sarauta da kuma mika ma Sarkin Gwantu sandar soma aiki. Bikin
nadin sarautar na Mai Martaba Sarkin Gwantu, Alhaji Balarabe Abdullahi Karma an
gudanar da shi ne a Gwantu dake karamar hukumar Sanga a kudancin Kaduna.
Tunda fari a cikin jawabinsa, gwamnan ya
fara ne da cewa, “Ku ba ni dama na fara da taya al’ummar masarautar Gwantu wadanda
lokuta da dama suka bayyana mana farin cikinsu kan yadda aka sake fasalin
tsohuwar masarautar Gwantu wanda ya yi sanadiyyar samar da masarautar Arak.
Gwantu tana da tsohon tarihi na tsawon shekaru fiye da dari, wanda gwamnatin
jihar Kaduna ta sake kafawa domin gyara wasu matsalolin mulki.
“A don haka muna yi wa al’ummar wannan
tsohuwar masarauta da Majalisar masarautar ta Gwantu fatan samun nasara wajen
ganin ta kasance daya daga cikin Masarauta mafi kyau a jihar, ta samu zaman
lafiya, hadin kai da kuma shiga ayyukan al’umma.” Inji Gwamnan.
“Muna taya Mai Martaba Alhaji Balarabe
Abdullahi Karma murna bisa nadin da aka yi masa a matsayin Sarkin Gwantu mai
daraja ta biyu, muna yi masa fatan alkhairi tare da yi masa addu’ar kammala
sarautar Gwantu da aikin jihar baki daya lafiya. An daukaka matsayinsa inda aka
dora masa wasu ayyuka masu yawa, wadanda suka wuce irin ayyukan da ake gani na
sarauta", in ji shi
Da yake yabawa Sarakunan gargajiya bisa
goyon bayan da suke bayarwa ta fannin tattara bayanan sirri domin shawo kan
kalubalen tsaro a jihar da kuma adana bayanai, gwamnan ya kuma bukaci daukacin
al’umma da masu ruwa da tsaki da su ci gaba da tabbatar da kyakkyawar alaka da
zaman tare, inda ya nemi kafatanin al’umma da su hadai kai domin tabbatar da an
gudanar da zaben 2023 cikin kwanciyar hankali.
Gwamnan ya ci gaba da cewa; “A yayin da
muke tunkarar zaben 2023, ina kira ga shugabanninmu na gargajiya, al’ummarmu da
kuma malaman addininmu da su ci gaba da wa’azi domin tabbatar da an gudanar da
‘yancin dimokuradiyya cikin lumana, a kwadaitar da duk wadanda suka cancanci
kada kuri’a su yi hakan cikin ’yanci, a cikin yanayin da babu tashin hankali ko
tsoratarwa.
“Kada ’yan siyasa su yi amfani da
matasan mu wajen tauye hakkin da tsarin mulki ya ba kowane dan kasa na zaben
jam’iyya da dan takarar da yake so. A bangarenmu, gwamnati za ta tabbatar da ta
bayar da tsaro domin bayar da damar da ‘yancin kada kuri’a ga masu zabe da
yardar Allah,” in ji El-Rufai.
Da yake mayar da bayani, Sarkin Gwantu
ya ce, “Ina so na tabbatar wa da mai girma Gwamna cewa, bisa ga salon mulkin ka,
manufata ga masarautarnan shi ne tabbatar da tsaro, zaman lafiya, hadin kai da
kuma mutunta al'adu da addinin juna.
“Wannan abu ne da kowa ya sani a duniya cewa;
tsaro, zaman lafiya da hadin kai su ne ginshikan da ke tabbatar da ci gaban
kowacce al'umma. A kan wannan tafarki ne ni, da mutanen masarautarnan za mu
tsara matakan da za mu bunkasa rayuwarmu domin cimma wadannan muradan”.
An haifi Sarkin Gwamnatu a ranar 31 ga
Maris, 1955 a Gwantu. Balarabe Abdullahi Karma, ya fito ne daga gidan mulki na
“Gbatun”.
A farkon rayuwarsa Balarabe Abdullahi
Karma ya sami ilimin addinin musulunci a garin Gwantu inda ya koyi Alkur'ani da
koyarwar Annabi Muhammad (S). Daga baya ya fara karatunsa na firamare kuma ya
kammala a shekarar 1969.
Ya yi digirinsa a bangaren tattara bayanai
kan laburare da halayyar dan Adam daga Jami’ar Bayero dake Kano, inda ya
kammala a 1988.
Karma wanda ya kasance Malami tsawon
rayuwarsa tun daga matakin firamare har zuwa makarantar sakandare har ma ya zama
shugaban Makarantar Sakandaren Gwamnati Gbonkok, Arak na farko.
A cikin 2002, aka canza masa wurin aiki
zuwa Ofishin yanki dake Anchau a matsayin mai kulawa. Ya kai har matsayin
Darakta a sashen tabbatar da inganci. Balarabe Abdullahi Karma ya yi ritaya
daga aiki a ranar 31 ga Maris, 2015, bayan ya shafe sama da shekaru talatin da
biyar (35) yana aikin gwamnati.
No comments