Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

7Gmedia Cooperative Ta Kone Tsintsiya Guda 1000 A Zariya

Daga Fatima Idris Zariya Taron kungiyar matasan jam'iyyar PDP da ake kiransu da 7Gmedia Cooperative na garin Samaru karamar ...


Daga Fatima Idris Zariya

Taron kungiyar matasan jam'iyyar PDP da ake kiransu da 7Gmedia Cooperative na garin Samaru karamar hukumar Sabon Gari ya samu karbuwa. Wakiliyarmu ya shaida yadda taron ya gudana.

Taron an gudanar da shi ne a babban Titin Malam Alumu mai kananzir dake tsakiyar garin Samaru. Kungiyoyin matasa ne daga mazabu daban-daban suka halarci wajen taron.

A bangare guda kuma iyayen jam'iyyar PDP na karamar hukumar Sabon Gari tare da yan takara ne suka marawa taron baya.

Bayan bude taron da addu'a ne aka bai wa manyan baki dama su fadi albarkacin bakinsu a matsayin Allah-san-barka ga kungiyar ta 7Gmedia Cooperative din.

Manyan bakin da 'yan takarar da suka gabatar da jawabai duk sun yi jawabansu ne akan karfafa matasa ne akan zabe mai tunkaromu na 2023.

Daga cikin wanda suka gabatar da jawabai akwai Kwamared Ibrahim Garba Umar wanda shi ya wakilci shugaban matasan jam'iyyar PDP na kasa baki daya Kwamared Kadade.

Akwai Honorabul Gambo shugaban jam'iyyar PDP na karamar hukumar Sabon Gari da Dan takarar kujerar majalisar jihar ta Kaduna mai wakiltar mazabar Basawa Honorabul mai Gidan ruwa da mutane da dama.

Bayan manyan baki su gabatar da jawabai dake kara kwarin guiwa tare da jajircewa a neman kare kuri'u yayin gudanar da zabe a fadin karamar hukumar kungiyar ta sami tallafi na kudi daga gurin manyan baki tare da yi wa kungiyar albishir na ba su wasu damarmaki kamar yadda ake ba sauran kungiyoyi a halin yanzu.

Bayan kammala taron 'ya'yan kungiyar sun bankawa tsintsiya guda 1000 wuta a bainan jama'a tare da Allah-wadai da halin da jama'a me ciki a wannan lokacin.

Haka zalika waliliyarmu ta zanta da shugaban kungiyar ta 7Gmedia Cooperative akan makasudin shirya taron na su. Kwamared Usman Audi shi ne shugaban kungiyar ta 7Gmedia Cooperative Samaru kuma ta tabbatar da cewa sun kafa kungiyar ne don wayar da kan matasa maza da mata har da iyaye baki daya.

Shugaban ya kara da cewa kungiyar tana karkashi jam'iyyar PDP ne, kuma suna sone su kawo canji a fadin karamar hukumar Sabon Gari baki daya.

Shugaban ya karkare da cewa su sun gaji da tura mota a bar su da shan hayaki don haka yanzu za su bayar da lokaci don wayar da kan matasa don kawo sauyi mai inganci da zai taimaki matasa da tsofaffi baki daya karkashin jam’iyyar PDP da ikon Allah.

Kwamared Arfat Muhammad ita ce wakiliyar 'yan matan 7Gmedia a na ta jawabin cewa ta yi a gaskiya yanzu kan mage ya waye hakan yasa kungiyarsu ta7Gmedia Cooperative ta fito da karfinta don samawa matasa mafita ta hanyar wayar masu da kai a siyasance karkashin PDP a karamar hukumar Sabon Gari da kasa baki daya.

Kwamared Arfat ta karkare da cewa mazansu da matansu ba za su yi kasa a guiwa ba wajen fadakar da mata muhimmancin zabe don samun 'yanci ga rayuwarsu, ta yi fatan duk wanda ya zo taron Allah ya mayar dashi gida lafiya.

No comments