Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

An Haramta Wa Lewandowski Buga Wasanni 3 A Laliga

  Dan wasan gaba na Barcelona, ​​Robert Lewandowski ba zai buga wasanni uku masu zuwa ba, bayan matakin ladabtar da shi da hukumar kwallon S...

 

Dan wasan gaba na Barcelona, ​​Robert Lewandowski ba zai buga wasanni uku masu zuwa ba, bayan matakin ladabtar da shi da hukumar kwallon Spain ta dauka, na haramta mishi wasannin, wanda kotun sauraron kararrakin wasanni ta Spain ta tabbatar.

An hukunta Lewandowski ne bayan da ya karbi katin gargadi na biyu, sannan kuma ya wuce gona da iri wajen nuna bacin ransa kan katunan da aka daga masa, a wasan da Barcelona ta buga da Osasuna a ranar 8 ga Nuwamba.

Amma bayan da Barcelona ta daukaka kara kan dakatarwar Lewandowski ya samu buga wasan da suka kara da Espanyol a karshen makon da ya gabata.

Da farko dai Kocin Barcelona Xavi Hernandez ya ce yana tsammanin dan wasan na Poland zai samu damar buga wasan da za su fafata da Atletico Madrid a ranar Lahadi, sai dai a yanzu dole ya zauna a benci

Kwallaye 13 Lewandowski ya zura a wasanni 15 da ya buga a gasar La Liga a bana.

No comments