*’Yan majalisa sun zama ‘yan amshin shata *Har yanzu talakawan kasarnan ba su san ina ke musu ciwo ba Wannan ita ce hirar da Babban Edit...
*’Yan majalisa sun zama ‘yan amshin shata
*Har yanzu talakawan kasarnan ba su san ina ke musu ciwo ba
Wannan ita ce hirar da Babban Editanmu, Ammar
Muhammad Rajab ya yi da matashin Malamin nan mai suna Malam Musa Gambo Yakana
wanda ke zaune a garin Zariya ta jihar Kaduna, kuma ya kasance mai sharhi ne
kan al’amuran yau da kullum. Mun tattauna da shi ne dangane da batun canjin
kudi da gwamnatin Muhammadu Buhari ta yi wanda al’umma a daidai wannan lokaci
suka fada halin tasku da kunci. Editanmu ya yi tattaki ne har zuwa gidansa ga
kuma yadda hirar ta kasance:
MADOGARA: al’umma na cikin baganniya kuma gwamnatin
Buhari ta dage akan wa’adin da ta kayyade na ranar 31 ga Janairu wanda daga nan
ba za a sake karbar tsohon kudi ba. Tare da neman al’umma su koma saye da
sayarwa ta hanyar wayoyinsu ko POS da kuma takaitattun sabbin kudi. Mene ne ra’ayinku
a kan wannan dagewar da gwamnatin Buhari ta yi duk da kiraye-kirayen da al’umma
ke yi mata?
MALAM MUSA: lallai
kam Buhari ba wannan mulki bane ya fara wannan bakin mulkin ba. Domin tun a
wancan lokacin da ya yi mulki, kusan duk lokacin da ya yi mulki ba wanda yake
yakarsu irin masu arziki. Kuma arziki ba wani ke yi ba, Allah ke yi. Duk wanda
ya ce yana yaki da wani ni’ima da Allah ya yi wa wani bawansa, to yana yi da Allah
(SWT). Lallai maganar wannan canjin kudin da Buhari ya kirkiro domin mu ba za
mu ce gwamnan CBN bane ya yi, domin gwamnan CBN yana karkashin Buhari ne.
Kowanne dan kasa yana karkashin Buhari ne domin shi ke da karfin mulki. To
Buhari haka a wancan karon ya tadawa da iyayenmu hankali ya ce a yi canjin kudi
kuma bisa rashin ka’ida. Ko ko don Buharin nan yana ganin kamar danginsa babu
masu arziki ne? Domin da da masu arziki lallai yakamata ya yi kishin danginsa.
To haka a wannan lokacin yana maimaici ne na wancan bakin mulkin.
Kuma bakin mulkin da
Buhari ya yi a wancan lokacin shi ta kai shi ga Babangida suka hambarar da shi
akan mulki. Domin bana mantawa saboda irin bakin mulkin da Buhari ya yi, haka
aka rika raba addu’o’i makarantu-makarantu da tsangayoyi akan Allah ya yi
maganin Buhari. Buhari yakamata ya dauki darasi a wancan mulkin.
Ko a wannan zaben sai
da aka tuna masa abubuwan da ya yi a wancan mulkin, ya ce wannan ai
dimokuradiyya ne, wancan soja ne. Ya yaudari al’umma, suka ce ai ya canja
wannan dimokuradiyya ne. Suna da ‘yan majalisu. Jama’ar kasarnan sun manta ‘yan
majalisu ‘yan amshin shata ne. Domin mafi akasari ‘yan majalisun nan karnukan farauta
ne. Iyakar idan an farauto a yi kaso mu raba da su. Da Buhari da ‘yan majalisu
Danjuma da ne da Danjummai. Buhari ka da ya manta ba yana mulkin dabbobi bane,
yana mulkin mutane ne. Kuma mutanan nan sune suka zabe shi. Ba a taba shugaba a
Afrika ko na ce a duniya wanda ya yi farin jinin Buhari ba, wanda talakawa suka
yi birgima suka ce ‘sai Baba Buhari mai adalci’, ashe ba su san macucinsu bane.
Su suna yi masa kallon macecinsu ne, ashe macucinsu ne. Mun dauka Buhari a
shekarunsa zai canza tunda yana kusantar lahira ne, amma Buhari sai ya kasance
giyar mulki na dibarsa. Iyayen gidansa Turawa suna amfani da shi wajen
musgunawa talakawansa.
Maganar canjin kudin
nan ‘yan majalisu suna ta magana wai za a kara wa’adi, a’a, ‘yan mashin shata
ne. Kuma mu muna la’akari wannan batu na canjin kudi magana ce ta satar kudi da
Gudaji Kazaure yake magana a kai. Domin mu a irin tunaninmu me yasa ba a tada
batun canjin kudi ba sai da Gudaji Kazaure ya tona biliyoyin kudin da aka diba
na sata. Kuma gwamnan CBN din nan ake zargi, kuma sai aka ce za su yi canjin
kudin nan. Tana iya yiwuwa sun kirkiro canjin kudin nan sun buga kudi da yawa,
wanda za su samu su maido da wasu kudi. Wannan canjin kudin da ake yi ba wani
abu bane bula ce aka sa. Ta yiwu kudaden da ke komawa bankuna na tsoffin kudi
za su tura ne maimaikon su buga wani kudi. Sai su tura su mayar da kudin CBN
sai su ce ga kudin da ake fadin gwamnan CBN ya sace bai sace ba, lallai
kirdadonmu ke nan.
MADOGARA: Allah ya gafarta Malam, al’umma dai wannan
karon sun hadu a kusan ra’ayi guda ana ta Allah-wadai da tir da gwamnatin
Muhammadu Buhari. Kana ganin wannan Allah-wadai da al’umma ke yi da kuka da na
sani da gaske suke ko kuma fadar fatar baki ne?
MALAM MUSA: Allah-wadai
da suke yi na fatar baki ne. Domin kamar yadda Buhari ya fito ya yi ta zagaye
yana cewa a zabe shi, kuma idan ya yi muku abin da ba ku yarda ba ku fito
gangami ku hau kan kwalta ku ce ba ku yarda ba. Ai ku yake mulki, to ga abin da
kuke so. Kamar yadda Buhari ya taba yi lokacin Jonathan ya fito ya jagoranci
zanga-zanga a kasarnan yake cewa ba su yarda da karin kudin man fetur ba.
Buhari ya yaudari mutane yana fadin taliya naira sittin (60) bai kamata ana
saya naira sittin ba, ashe ya kwantar da mutane ne yana jiran ba naira sittin
ba, taliya ta koma naira dari shida ne. Maimakon naira sitti yanzu taliya ta
koma wajen naira dari shida.
Kuma a halin da ake
ciki talakawan kasarnan har gobe ba su san me suke yi ba. Domin za mu ce gwanda
dabbar daji da talakawan kasarnan. Domin dabban daji idan an cutar da ita yau,
gobe wallahi idan ta ganka ba ta barinka sai ta dauki mataki. Amma su talakawan
kasarnan su kan zauna ne su shantake. Hatta a midiya ma ba magana, suna tsoro. Mene
ne? Idan an kama ko an halaka ka, ai akan gaskiya ne. Kumai ta gwagwarmaya duk
duniya ba ta taba samun ‘yanci ba sai da gwagwarmaya. Duk duniya domin kamar
ita kanta ‘yancin kan ma da ake magana ai gwagwarmaya aka yi. Amma sai ya
kasance su su Buhari sun mayar da ‘yan kasarnan yadda ka san silifas tsoho.
Abin da suke so suke yi. Ka ce ba dimokuradiyya ake yi ba, don Buhari salon
mulkinsa soja ne. Mulkin sojan ma bakin mulkin zalunci irin wanda ya taba yi a
shekarun baya.
MADOGARA: a
daidai wannan lokaci me kake ganin yakamata al’ummar Nijeriya su yi?
MALAM MUSA: to
da farko dai tsadar rayuwa ta yi yawa. Ba ma a kan canjin kudi ba. Tun kafin ma
canjin kudi ana cikin tsadar rayuwa. Al’ummar kasa su tashi mu nemi ‘yancin
kanmu. Domin idan muka bar mutanen nan suna cin karensu ba babbaka, wanda zai
hau shima haka zai dora, amma idan muka dauki mataki akan abin da suke yi mana,
gobe wanda zai zo dole zai gyara saboda ya san abin da ya gabata da na gaba da
shi. Amma irin wannan zaman da muke yi, ba su ma, ku san mun mutu ne, saura
kadan, dan wushisshiri muke yi kadan ya rage a kai mu kabari.
No comments