Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Dan Majalisar Tarayya, Babawo Ya Bayar Da Tallafin Magani Kyauta A Karo Na 8 A Zariya

Daga Sayyada Adam Zariya Dan takarar kujerar majalisar tarayya mai wakiltar karamar hukumar Sabon Gari a jihar Kaduna, Honorabul...


Daga Sayyada Adam Zariya

Dan takarar kujerar majalisar tarayya mai wakiltar karamar hukumar Sabon Gari a jihar Kaduna, Honorabul Garba Datti Babawo ya kaddamar da aikin bayar da tallafin magani kyauta tare da bai wa wasu asibitoci kayan aiki don karfafa kiwon lafiya a fadin karamar hukumar ta Sabon Gari.


A lokacin da yake kaddamar da aikin bayar da tallafin maganin Dan majalisar ya tabbatar da cewa zuwa yanzu shirin bayar da tallafin ya yi wa masu lalurar ciwon kaba (Fibroids) kimamin mutum 1, 277 tiyata kuma duk an sami nasara yin aikin.

Haka zalika Dan majalisar ya tabbatar da cewa shirin ya duba mutane masu fama da maleriya da Typhoid da sauran ciwuka fiye da mutum 25, 259 a fadin karamar hukumar ta Sabon Gari baki daya.

Kuma ya kara da cewa a wannan karon ya kawowa bulabban asibitin Mejo Ibrahim Abdullahi Memorial Hospital (LIMI HOSPITAL) kayan gudanar da aiki a cikin Asibitin na Naira miliyan 30 don amfanar mutanen karamar hukumar ta Sabon Gari da jihar Kaduna baki daya.

Karshe ya yi fatan al'ummar karamar hukumar za su kara bashi goyon baya don karashe aikin da ya dauko yi a bangarori da dama a zabe mai tahowa. 

Daga cikin manyan baki da suka rufawa taron kaddamar da bayar da tallafin maganin baya sun hada da Honorabul Yusuf Shaka da Honorabul Abubakar Albani da Honorabul Nasiru Idi Kano da Malamai da Sarakuna da wakilan sashen lafiya na kananan hukumomi da 'yan takarkaru da sauran manya manyan 'yan  jam'iyyar APC duk sun tofa albarkacin bakinsu da ya nuna goyan baya ga Honorabul Garba Datti Babawo akan kokarin da yake yi wa al'ummarsa karshe sun nemi goyan bayan jama'a don karasa abin alherin da yake gudanarwa a fadin karamar hukumar baki daya.


Binciken da jaridar MADOGARA ta yi shi ne wani sakamako bayar da tallafin maganin zai bayar a halin yanzun?

Binciken ya tabbatar da cewa bayar da tallafin maganin a irin wannan lokaci da yanayi da ake ciki na wahalar rayuwa zai taimakawa siyasar Dan majalisar ta kowani bangare ganin yadda magani ya yi karanci a asibitocin gwamnati kuma ya yi tsada a asibitocin masu zaman kansu domin a yanzu yin tiyata ga mara lafiya ba karamin tashin hankali bane wanda haka yasa da yawa suke rasa ransu bisa rashin kudin maganin ko kudin yin tiyata din domin komin kankantar tiyata akan caji kudi mai yawan gaske ne a asibitocin gwamnati da na 'yan kasuwa.

Bincike ya tabbatar cewa bayar da wannan tallafi da Dan majalisar ke yi yana karawa jam'iyyarsa ta APC farin jini duk da matsin lamba da jam'iyyar ke sha a wajen mutane.

Shugaban ayarin likitocin dake karkashin ayarin Doctor on the move Africa, Dakta Kagbu a jawabinsa ya tabbatar da cewa in Allah ya so za su yi aikinsu cikin nasara damar za a ci gaba da ba su goyan baya kamar yadda aka saba a lokutan baya ya tabbatar da cewa daruruwan mutane ne za su sami tiyata a bangarori daban-daban bayan an gama masu gwaje-gwaje da ikon Allah.

Honorabul Injiniya Muhammad Usman shi ne shugaban karamar hukumar Sabon Gari shi kuma godiya ya yi ga Dan majalisar nasa bisa kokari da yake yi a bagarori da dama ya ce da 'yan siyasa za su yi koyi da abin da Honorabul Babawo yake yi to da an sami ci gaba sosai a cikin siyasar kasar. Ya yi masa fatan alheri kuma ya nemi goyan bayan jama'a wajen mara masu baya a zabe mai tahowa.

No comments