Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Dan Takarar Shugaban Ƙasa A AAC, Sowore Ya Dira A Kano Domin Kulla Alaka Da PRP

Dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar African Action Congress (AAC), Mista Omoyele Sowore  ya isa Kano a jiya Lahadi domin guda...


Dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar African Action Congress (AAC), Mista Omoyele Sowore  ya isa Kano a jiya Lahadi domin gudanar da shirye-shiryen taron jam’iyyar People’s Redemption Party na Arewa maso Yamma da aka shirya gudanarwa a yau Litinin 16 ga watan Janairu, 2023.

Za a gudanar da taron ne domin nuna goyon baya ga tikitin Sowore/Magashi, da kuma haɗin gwiwa tsakanin jam'iyyun siyasa biyu - AAC da PRP.

Idan za a iya tunawa a baya can a wani taron jam’iyyar PRP da aka gudanar a yankin Arewa maso Gabashi a jihar Gombe jam'iyyar PRP ta bayyana goyon bayanta ga dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar AAC, Mista Omoyele Sowore. Hakan ya biyo bayan wani taron manema labarai na hadin gwiwa na jam’iyyun siyasa biyu masu hade da juna a sakatariyar NUJ da ke Abuja.

Haka kuma ana sa ran halartar shugabannin Arewa maso Yamma na African Action Congress da wasu manyan jami'an AAC.

No comments