Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamnatin Zamfara Ta Ce Ta Gano Likitocin Bogi 169, Ta Ce 81 Kawai Na Gaske

Daga Hussaini Gusau Gwamnatin jihar Zamfara ta bayyana cewa ta gano wasu likitocin bogi guda 169 da ke cikin kundin biyan albash...


Daga Hussaini Gusau

Gwamnatin jihar Zamfara ta bayyana cewa ta gano wasu likitocin bogi guda 169 da ke cikin kundin biyan albashin da aka gano yanzu haka..

Gwamna Bello Mohammed Matawalle ya bayyana hakan ne a zantawarsa da manema labarai a Maradun.

Gwamna Matawalle ya bayyana cewa, gwamnatinsa na biyan albashi ga likitoci 250 duk wata, ya kara da cewa gwamnatin jihar ta gano likitoci na gaskiya 81 ne kawai ke aiki.

Ya kara da cewa, “Gwamnatin jihar Zamfara tana da likitoci 81 ne kacal a farko saninsa kuma daga cikin likitocin 169 an saka su a cikin albashin jihar ta hanyar magudi, shi ne wa kawo tsaikon biyan albashin Likitocin.

Ya kuma bayyana cewa, tuni ya gana da jami’an kungiyar kwadago ta kasa (NLC) reshen jihar kan yadda za a gano wadancan likitocin bogi 169 da suka dauki tsawon lokaci suna karbar albashi ba bisa ka’ida ba inji gwamna Matawalle. 

“Kungiyar Kwadago ta tabbatar min da cewa dalilin da ya sa aka jinkirta biyan albashin ma’aikatan lafiya shi ne, suna son tabbatar da cewa lamarin sun tafi daidai kuma nan ba da jimawa ba za mu magance dukkan matsalolin a bangaren lafiya”, a cewar Matawalle.

"Matawalle ya biya albashin watan Nuwamba da Disamba ga dukkan ma’aikatan lafiya amma abin takaici mun gano cewa muna da likitoci 81 kacal amma abin takaici a cikin albashin likitocin mu muna biyan albashin likitoci 250 duk wata, don haka dole ne mu cire wadannan likitocin bogi 169 daga cikin albashin mu", inji shi. 

Matawalle ya bayyana cewa, gano likitocin bogi ya biyo bayan ci gaba tantance duk ma'aikatan jihar ta hanyar ofishin shugaban ma'aikatan jihar da gwamnatin jihar ta yi na fara aiwatar da N30, 000 yadda ya kamata. 

Wakilinmu ya ruwaito cewa gwamna Bello Mohammed Matawalle ya dauki karin ma’aikatan lafiya 500 aiki, ya gina asibitocin kula da lafiya na matakin farko a daukacin Anguwanni 741 dake fadin jihar.

Ya kuma ba da tabbacin cewa babu wani ma’aikaci na gaskiya da gwamnatinsa za ta ki biyansa albashi.

“Ba zan kori duk wani ma’aikaci da gwamnatin jihar ta dauka na gaskiya ba. A kan haka amma za mu tabbatar da tsaftar ma’aikata kamar yadda doka ta tanada domin mu samu damar aiwatar da mafi karancin albashi na Naira dubu 30 yadda ya kamata", ya jaddada. 

Ya kuma kara da cewa, gwamnatinsa za ta kara himma wajen tabbatar da samar da kiwon lafiya ga daukacin al’ummar jihar idan aka sake zabensa a karo na biyu a karkashin jam’iyyar APC.

"Za mu kara yin aiki tukuru don ganin cewa ingantaccen aikin bayar da lafiya ga jama'armu a zango na biyu da yardar Allah". in ji Matawalle .

No comments