Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Hanyar Kaduna Zuwa Kano Ta Tsaya Cak Sakamakon harbe Direban BUA da Soja Ya Yi Kan Naira 300

           Hoto: Hajara Bukar Daga Ammar M. Rajab Labarin dake shigowa Jaridar MADOGARA na nuni da cewa wani soja ya harbe direb...

           Hoto: Hajara Bukar


Daga Ammar M. Rajab

Labarin dake shigowa Jaridar MADOGARA na nuni da cewa wani soja ya harbe direban kamfanin BUA a titin Kaduna zuwa Kano, lamarin da ya sanya direbobin manyan motoci tare babbar hanyar tun jiya har ya zuwa hada wannan rahoton. 

Lamarin ya faru ne da safiyar jiya Laraba 11 ga watan Janairun 2022 a daidai wani gari da ake kira Wambai. Ganau sun shaida mana cewa sojan ya nemi direban ya ba shi cin hanci na naira 500 inda direban ya ki bayarwa, sai dai ya ba shi naira dari 200 kyauta ya ki cika masa naira 300 ya zama naira 500, sojan nan take ya harbe direban ya kashe shi.

Wannan aika-aikar na sojan ya fusata al'umma da dama inda tun safiyar jiya direbobin manyan motoci suka rufe hanyar har ya zuwa hada wannan rahoton a yau Alhamis 12 ga Janairu babu wani motsin ababen hawa dake tafiya. Ganau sun ce da yawan matafiya zuwa Kano a hanya suka kwana saboda babu hanyar ratsawa a wuce.

Ya zuwa hada wannan rahoton babu wani takamaimen bayani daga hukuma ko rundunar soja.

Matafiya da dama na ta tofin Ala ya tsine ga wannan soja da rundunar sojin Nijeriya bisa abin da jami'inta ya aikata. 

No comments